Mai girma ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari da gwamna Nasir Idris sun kaddamar da shirin bunkasa noma mai taken KADAGE a Karamar Hukumar Suru da ke Jihar Kebbi.
A shirin an raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana da injinan wutar lantarki ga manoma a karkashin shirin bunkasa noma da ci gaban mai taken KADAGE.
A cewar ministan, Shugaba Bola Tinubu, ya himmatu wajen inganta harkar noma da kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan daidai da ajanda takwas na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
“Shugaba Tinubu ya sanya batun samar da abinci na daya a cikin ajandarsa takwas ta hanyar inganta noma a kasar nan.
“Dukkan shirye-shiryen da ke cikin ajandar na da alaka da noma, kamar samar da arziki da kawar da fatara da bunkasa tattalin arziki.
“Shugaban kasa ya damu da yadda manoma za su iya samun kayan aikin noma kuma a yanzu ya fara wani tsari na hanzarta samar da irin wadannan kayan amfanin gona ga manoma,” in ji shi.
Sanata Kyari, ya sanar da taron cewa Gwamna Nasir Idris ya kai ziyara a ofishinsa da ke Abuja domin tattauna hanyoyin inganta noma a jihar.
“Ta hanyar ayyukan Gwamna Idris, ya ‘tattaki zance’ ta hanyar sayo da raba famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 6,000 da sauran kayan aiki don bunkasa noman ban
ruwa a jihar,” in ji shi.