Kamfanin Dangote (DIL) ya zargi Kamfanonin Mai na ƙasa da ƙasa (IOCs) da ke aiki a Najeriya da laifin kawo cikas ga ayyukan matatar man Dangote da gangan ta hanyar ƙara farashin ɗanyen man da ake samu a cikin gida.
Mataimakin shugaban kamfanin matatar man da iskar gas na DIL, Devakumar Edwin, ya bayyana hakan ne a wani taron horas da ‘yan jarida masu samar da makamashi, inda ya zargi hukumar IOC da neman kuɗaɗen da ya wuce kima ko kuma cewa babu ɗanyen mai, wanda hakan ya tilastawa matatar Dangote biyan ƙarin Dala 6 sama da farashin kasuwa a lokaci guda.
Fara Aikin Matatar Dangote Da Ta Fatakwal: Jama’a Na Dokin Karyewar Farashin Fetur
Duk da ƙoƙarin da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ke yi na ganin an cika wajibcin samar da ɗanyen mai a cikin gida (DCSO), Edwin ya ba da shawarar cewa IOCs na lalata wannan yunƙurin.
Ya kuma jaddada cewa, NUPRC ta himmatu wajen cimma wannan ƙuduri, inda ya yi tsokaci kan taron da suka yi a baya-bayan nan da masu samar da ɗanyen mai da masu matatun man don aiwatar da dokar da ta kafa dokar masana’antar mai (PIA).
Edwin ya zargi IOCs da yunƙurin yin zagon ƙasa ga nasarar da matatar ta samu, wanda hakan ya tilastawa matatar da Dangote ya nemo ɗanyen mai daga wurare masu nisa da tsada kamar Amurka.
DUBA NAN: Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Katsalandan A Al’amuran Kano
Wannan lamarin yana ƙara ta’azzara tsadar kayan aikin matatar tare da kawo cikas ga aikinta.