Matatar Dangote ta karbi danyen mai karo na hudu har ganga miliyan daya daga kamfanin man fetur na kasa (NNPC).
A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Lahadi, matatar ta Dangote ta ce tana sa ran samun danyen mai karo na biyar da za ta tace.
“Shirye-shiryen fara samar da mai a matatar Dangote na ci gaba da tafiya.
Mun karbi danyen mai karo na hudu, ganga miliyan daya daga NNPCL kuma muna tsammanin karbar karo na biyar nan gaba kadan,” in ji kamfanin.
Dangote ya bayyana cewa da zarar matatar ta karbi jimillar ganga miliyan shida, za ta fara samar da man dizal, man jirgin sama, gas da kuma man fetur.
A cewar sanarwar, Manajan Daraktan Ayyukan wannan matata ta Dangote, Akin Omole, ya sanar da ‘yan jarida cewa matatar ta yi hasashen samun kusan miliyan hudu a karshen shekarar 2023.
Matata na sa ran karbar ganga miliyan biyu na danyen mai a farkon watan Janairun 2024.
A ranar 8 ga watan Disamba, 2023, Dangote ya sanar da karbar kashin farko na ganga miliyan daya daga kamfanin Stasco.
Haka kuma, a ranar 20 ga watan Disamba, 2023, matata ta karbi kashi na biyu na danyen mai daga NNPC.
A ranar 29 ga watan Disamba, 2023, matata ta Dangote ya ta sake karbar kashi na uku na ganga miliyan daya na danyen mai.

Source: LEADERSHIPHAUSA