Majalisar Dokokin Jihar Zamfara dake Najeriya ta dakatar da mambobin ta guda biyu da ake zargin suna mu’amala da ‘Yan bindigar da suka hana zaman lafiya a jihar.
Daraktan hulda da ‘Yan Jaridu na Majalisa din Mustapha Jaafaru Kaura yace ‘Yan Majalisun guda biyu zasu kauracewa zaman Majalisar na watanni 3 har zuwa lokacin da za’a kammala bincike akan su.
Kaura yace tuni aka baiwa kwamitin da’a na Majalisar umurnin gudanar da bincike akan su tare da hukumomin tsaron jihar kamar yadda zaman Majalisar ya amince.
‘Dan Majalisa Yusuf Alhassan Kanoma ya gabatar da bukatar daukar mataki akan ‘Yan Majalisun guda biyu wadanda yace suna murna lokacin da ‘Yan bindiga suka kama mahaifin shugaban Majalisar Alhaji Muazu Abubakar Magarya.
Kanoma ya kuma zargi ‘Yan Majalisun guda biyu da hannu wajen kashe tsohon ‘dan majalisa dake wakiltar Shinkafi Muhammad G. Ahmad wajen tseguntawa Yan bindiga bayanan tafiyar sa domin hallaka shi.
‘Dan Majalisar dake wakiltar mazabar Birnin Magaji Nura Dahiru Sabon Birni Dan Ali ya goyi bayan kudirin, inda yace duk yunkurin da akayi na kubutar da mahaifin Kakakin Majalisar daga hannun Bello Turji yaci tura.
Tuni Majalisar ta tube mutanen biyu daga shugabancin kwamitocin ta, yayin da aka fara bincike akan su.
A wani labarin na daban ‘yan bindiga a Najeriya sun hallaka akalla mutane 24 a wasu jerin hare hare da suka kai Jihohin Zamfara da Katsina dake fama da matsalar tsaro.
Rahotanni sun ce a ranar talata ‘yan bindigar sama da 100 akan babura sun yi wa kauyen Kuryan Madaro kawanya, inda suka kashe mutane da dama tare da kwace wayoyi da kudaden su.
Kakakin ‘yan sandar Jihar Katsina Gambo Isah ya ce wasu ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Yasore da ke Batsari inda suka hallaka mutane.
Jihohin Zamfara da Katsina na daga cikin yankunan da ‘yan bindiga suka fi kai munanan hare hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya.