A ranar Talata 26 ga Satumba, 2023 Majalisar Dattawa za ta tantance Dakta Olayemi Michael Cardoso, a matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Majalisar za ta kuma tantance mutane hudu da aka mika sunayensu ga majalisar a matsayin mataimakan shugaban Bankin CBN, wadanda kuma za su kasance a matsayin Kwamitin Gudanarwa da tafiyar da harkokin babban bankin har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
A cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na shugaban majalisar dattawa, Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya fitar a yammacin ranar Litinin, majalisar za ta tantance dukkan wadanda aka mika sunayensu ga majalisar bayan ta dawo hutun shekara a ranar Talata.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, a ranar 15 ga watan Satumba ne shugaba Tinubu ya amince da nadin Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin kasa (CBN).
Ya kuma amince da nadin mataimakan gwamnan su hudu na tsawon shekaru biyar kowanne a matakin farko in sun samu amincewar majalisar dattawa.
A wani labarin na daban wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a filin hoki da ke babban birnin Kano, ta umarci Abubakar Ibrahim da aka fi sani da G-Fresh, da ya koma gida ya shirya zuwa wajen bikon matarsa da ta yi yaji.
Kotun wadda ta bayyana cewar, tunda shi G-Fresh bai saki matarsa ba, akwai bukatar ya yi bikon ta domin cigaba da zaman aurensu.
Lauyar G-Fresh, Barr Fatima Aliyu ta bayyana cewa, har yanzun wanda ta ke karewa na matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ba zai iya rabuwa da ita ba.
Kotun dai ta umurci G-Fresh 25 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba da ya sulhunta da matarsa, Sayyada Sadiya Haruna.
Source: LEADERSHIPHAUSA