Ofishin firayi ministan kasar Iraki ya fitar da bayanin cewa, Macron tare da rakiyar firayi minista Alkazimi da kuam sauran jami’an da suke tare da su sun ziyarci hubbarori biyu na Imam Kazim da Imam Jawad (AS).
Wannan na zuwa ne bayan kammala taron da aka gudanar a jiya a kasar Iraki wanda ya samu halartar shugabannin kasashe da manyan jami’ai, kan tabbatar da zaman lafiya da yin aiki tare tsakanin kasashen yankin.
Shugaban kasar ta Faransa yana daga cikin wadanda suka halarci wannan zaman taro, inda aka tattauna batutuwa da dama da suke ci ma yankin gabas ta tsakiya tuwo a kwarya.
Masu lura da lamurran siyasa dai na ganin ziyarar hubbaren Imam Musal Kazim (S.A) din da aka kyale emannuel macron yayi a matsayin abinda ba zaiyi wa da dama daga cikin musulmi dadi ba musamman duba da cewa shugaban kasar ta faransa na cikin na gaba gaba wajen goyon bayan masu ayyukan batanci ga shugaban halitta annabi muhammad (s.a.a.w.w), wanda hakan yake nuna rashin dacewar bashi dama ya halarci manyan gurare masu muhimmanci da tsarki da musulmi.
Idan ba’a mance ba a watannin baya aka samu wadansu shakiyyai a kasar ta faransa inda suka wallafa wani zanen batanci ga annabi muhammad (s.a.w.w) amma shugaba macron bai dauki mataki ba duba da yawan mabiya da annabin rahama (s.a.w.w) yake dasu a kasar da faransa dama fadin duniya wanda taba darajar sa ya sabawa tanadin dukkan dokokin kasa da kasa.