Masu zanga-zanga sun mamaye babban bankin CBN reshen jihar Edo saboda rashin samun damar sauya tsoffin kudinsu zuwa sabbi.
Sun bayyana cewa bankunansu sun umurce su da su garzaya CBN yayin da babban bankin ya nemi su koma zuwa bankunansu don sauya tsoffin kudin da sabbi.
Zanga-zangar na zuwa ne yan awanni bayan gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya sanar da cewar babu gudu babu ja da baya a wa’adin 10 ga watan Fabrairu.
Wasu yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a babban bankin Najeriya (CBN) reshen Benin, babban birnin jihar Edo, kan rashin samun damar sauya tsoffin kudinsu na N200, N500 da N1,000 zuwa sabbi.
A cikin bidiyon, masu zanga-zangar sun yi zargin cewa bankunansu sun umurce su da su tafi CBN idan suna son sauya tsoffin kudadensu da sabbi, sannan shi kuma CBN ya umurce su da su koma bankunansu.
Sun koka cewa manufar babban bankin na kuntata masu sosai, kuma akwai bukatar gwamnati ta daidaita tashin hankali domin abun dariya ne cewa suna da kudi a hannunsu amma ba za su iya amfani da shi ba.
Gwamnan CBN ya ce wa’adin 10 ga watan Fabrairu na nan na daina amfani da tsoffin kudi Zanga-zangar na zuwa ne jim kadan bayan gwamnan na CBN, Godwin Emefiele, ya yi watsi da hukuncin kotun koli sannan ya sanar da cewar wa’adin daina amfani da tsoffin kudin na nan daram-dam.
A ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, kotun koli ta zartar da hukuncin wucin gadi inda ta dakatar da gwamnatin tarayya daga hana yan Najeriya amfani da tsoffin kudin, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta bi umurnin kotun.
Sai dai kuma, yan Najeriya da dama sun kadu lokacin da suka ji Emefiele yana ayyana cewa wa’adin 10 ga watan Fabrairu na nan daram-dam na daina amfani da tsoffin kudin.
Gwamnan CBN ya yi wata ganawar sirri da Buhari kan batun NairaKowa ya yi transfa:
Kirjin biki ta fito da sabon salon karbar kudin liki
A gefe guda, yayin da yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar rashin tsabar kudi a kasar, wata uwar biki ta samawa kanta mafita don kada ta tashi a tutar babu.
Matashiyar dai ta nemi takarda sannan ta rubuta lambar akant dinta inda ta bukaci duk mara tsaba a hannu na liki ya yi mata transfa zuwa asusunta.
Source:LegitHausa