Gaza (IQNA) Bidiyon kiran sallar da aka yi kan rugujewar wani masallaci a Gaza ya samu karbuwa daga masu amfani da yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Reuters cewa, ma’aikatar ba da wa’azi ta zirin Gaza ta sanar da cewa, an rusa masallatai da dama a wannan yanki sakamakon harin bama-bamai da gwamnatin yahudawan sahyuniya ke kaiwa tun farkon yakin guguwar Al-Aqsa.
A makon da ya gabata ne ofishin yada labarai na jihar Gaza ya sanar da lalata masallatai 31 da majami’u uku.
A baya-bayan nan, wani faifan bidiyo da aka yi a ranar 29 ga watan Nuwamba, wanda ke nuna wani matashi yana addu’a kan rugujewar wani masallaci a Gaza, ya dauki hankula. Wannan faifan bidiyo ya nuna irin barnar da hare-haren da Isra’ila suka kai a harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba. A cikin wannan faifan bidiyo, wani matashin muezzin sanye da hular wasan baseball yana kiran mutane zuwa ga salla daga saman wani masallaci da aka kai hari a Gaza.
Wannan masallacin da ke garin Khan Yunus na daya daga cikin masallatan Gaza da Isra’ila ta kai wa hari a lokacin yakin. Isra’ila ta zargi Hamas da yin amfani da masallatai don dalilai na soji. Hamas dai ta musanta hakan, ta kuma zargi Isra’ila da kai hari a wuraren ibada da suka hada da masallatai da majami’u.
Fiye da Falasdinawa 15,000 galibi mata da yara ne aka kashe a yankin Gaza da aka yi wa kawanya sakamakon munanan hare-haren da gwamnatin Sahayoniyya ke yi.
Source: https://iqna.ir/ha/news/3490241/kiran-sallah-daga-wani-masallaci-da-israila-ta-ruguje-a-gaza