Wasan Arsenal da Wolves a gobe talata zai zama wasa na 15 da zuwa yanzu hukumar gudanarwar Firimiya ta dage zuwa wani lokaci daban saboda tsanantar cutar covid-19.
Zuwa yanzu ‘yan wasa 13 da mai tsaron raga guda ne suka harbu da corona.
Ko a jiya lahadi firimiyar ta dakatar da wasan Wolves guda wanda ke jerin wasannin 3 da ba a iya dokawa a jiyan ba, wato bayan na Liverpool da kuma Watford.
Duk da matakin karuwar masu coronar dai kungiyoyin firimiyar sun yi watsi da shawarar dakatar da kakar wasan da ake ciki zuwa wani lokaci na daban a nan gaba, don rage yaduwar cutar tsakanin ‘yan wasa.
Kungiyoyin dai sun tsaya kan matsayar cewa matukar kowacce kungiya na da ‘yan wasa 13 lafiyayyu da kuma mai tsaron raga to wasanni za su ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara.
A wani labarin na daban Hukumar UEFA ta sanar da dakatar da wasan Tottenham da Rennes yau alhamis karkashin gasar Europa Conference league bayan 8 daga cikin ‘yan wasan kungiyar ta Tottenham sun harbu da cutar corona.
Sai dai Rennes ta Faransa da ke shirin yin tattaki zuwa London tun a jiya ta sanar da matakin na Tottenham dangane da dakatar da wasan a matsayin batu mai rikitarwar.
Amma kuma sanarwar hukumar UEFA ta yau ta amince da dakatar da wasan zuwa wani lokaci a nan gaba ko da ya ke sanarwar ta ce matakin na Tottenham ya sanya ta a tsaka mai wuya.
Acewar UEFA sai a nan gaba ne za ta sanar da mataki na gaba kan yadda wasan kungiyoyin zai gudana, la’akari da cewa a ranar 31 ga watan nan na Disamba ne ake saran Karkare wasannin rukuni na gasar.
Akwai dai yiwuwar Tottenham ta bukaci dakatar da wasanta da Brighton karkashin gasar firimiyar Ingila.