Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya tace kofa a bude take ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan idan ya yanke hukuncin barin sa PDP domin sauya sheka zuwa cikin ta.
Sakataren yace duk lokacin da Jonathan ya yanke hukunci komawa Jam’iyyar APC zasu bashi matsayin da ya dace da shi na tsohon shugaban kasa, kuma jigo a cikin ta.
Akpanudoedehe yace taron shugabannin jam’iyyar na kasa da akayi ya bude kofa ga duk wani mai bukatar sauya sheka da ya koma ba tare sanya wani shinge ba.
Rahotanni sun ce komawar Jonathan na iya bashi damar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 domin yin wa’adi na biyu, sakamakon hana shi samun nasara a zaben shekarar 2015 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kada shi.
Ana dai ci gaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yayan jam’iyyar APCn dangane da wanda ya dace ya tsaya takarar zaben shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar.
Yayin da wasu ke cewa ya dace yankin arewacin kasar ya cika alkawarin da ya dauka wajen marawa jagoran jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu baya kamar yadda shima ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, wasu na cewa a bar kofa a bude ga duk wani ‘dan takara ya fito ya nemi kujerar ba tare da sanya sharudda ba.
Masu sanya ido akan harkokin siyasa na hasashen cewar matsalar fidda ‘dan takara a zabe mai zuwa na iya sanya jam’iyyar APC ta rasa kujerar shugabancin Najeriya.
A makwannin da suka gabata, Gwamnonin PDP da wasu shugabannin ta sun gargadi tsohon shugaban kasar akan barin domin komawa APC
Tun daga yanzu dai alamu suna nuna an fara kada gangar siyasar 2023, jam’iyyu kuma sun fara zawarcin ‘yan siyasa a lunguna da sakuna.