A ranar Talatar da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya tabbatar da zababben shugaban kasar a matsayin sabon shugaban ƙasa, a yammacin jiya Alhamis, sabon shugaban ƙasar Iran Dakta Sayyid Ibrahim Ra’isi ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Iran na takwas.
Wannan bikin rantsuwar kama aikin dai wanda aka gudanar a Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ɗin ya samu halartar manyan-manyan jami’an ƙasar ta Iran bugu da ƙari kan jami’ai da wakilai daga ƙasashe daban-daban na duniya da suka fito daga ƙasashe sama da tamanin.
An buɗe taron ne dai da jawabin shugaban majalisar shawarar Musulunci ɗin Muhammad Baƙir Qalibaf wanda a cikin jawabin nasa ya bayyana muhimmancin yin aiki tuƙuru wajen magance matsalolin da ƙasar ta ke fuskanta ba tare da neman wani uzuri ba.
Shugaban majalisar ya ce yayi amanna da cewa lalle Iran tana da ƙarfin da za ta iya magance matsalolin da take fuskanta yana mai jaddada ƙudurin majalisar na ba wa sabuwar gwamnatin haɗin kai wajen cimma burinta na magance waɗannan matsalolin.
Shi ma a nasa ɓangaren shugaban ɓangaren shari’a kana kuma alƙalin alƙalai na Iran Sheikh Gholam Husain Muhsin Ejei ya jaddada wajibcin yin hidima wa al’ummar Iran sakamakon tsayin dakan da suke yi wajen riƙo da tafarkin juyin juya halin Musulunci na ƙasar yana mai sanar da aniyar ma’aikatarsa ta shari’a wajen ba wa sabuwar gwamnatin haɗin kai wajen faɗa da rashawa da cin hanci da nuna bambanci.
Daga nan kuma sai ya jagoranci sabon shugaban wajen yin rantsuwar kama aikin.
Takardar rantsuwar kama aikin dai ta ƙumshin rantsuwar kiyaye adddinin Musulunci, tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kundin tsarin mulkin ƙasar bugu da ƙari kan haƙƙoƙin al’ummar ƙasar da kuma mutumcinsu bugu da ƙari kan yi musu hidima da kuma alƙawarin miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa idan wa’adin mulkin shugaba mai ci ɗin ya ƙare.
Daga nan kuma sai sabon shugaban ƙasar ya gabatar da jawabinsa.
Taron dai ya samu halartar tsohon shugaban ƙasar ta Iran Dakta Hasan Rouhani da ‘yan majalisar ministocinsa, bugu da ƙari kan manyan jami’ai na siyasa da na soji.
Tawagogi daga kasashe tamanin ne suka halartar taron rantsar da sabon shugaban kasar na Iran, da suka hada da shugabannin kasashe da na gwamnatoci, ministoci, shugabannin majalisun dokoki na kasashe daban-daban.
Sannan baya ga haka kuma wakilan majalisar dinkin duniya da kuma wasu wakilai daga kungiyouyi daban-daban na kasashen turai da Asia da Afirka da kuma latin Amurka suna daga cikin wadanda suka samu halartar taron, kamar yadda babban sakataren kungiyar kasashe masu fitar da danyen man fetur a duniya Alh. Sanusi Barkindo yana daga cikin mahalarta taro.