An kaddamar da shirin horas da daliban dake koyon ilimin fasahohi daban daban mai lakabin “Luban workshop”, a jami’ar IPRC Musanze dake arewacin kasar Rwanda.
Shirin na hadin gwiwa tsakanin jami’ar ta IPRC da kwalejin horas da fasahohi ta Jinhua dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, na da manufar bunkasa ilimin fasahohi, da koyon sana’o’i tsakanin daliban Rwanda.
Da take tsokaci kan shirin yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, mataimakiyar shugaban jami’ar ta IPRC madam Sylvie Mucyo, ta ce shirin na “Luban workshop” na kunshe da fasahohin zamani da duniyar yau ke bukata. Kaza lika shirin wata babbar nasara ce duba da cewa zai taimakawa daliban Rwanda wajen samun ilimi mai nagarta, da horo mai inganci cikin kyakkyawan yanayi.
Mucyo ta kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin jami’ar Rwanda da kwalejin Jinhua, zai ba da damar yin musayar kwarewa, ta yadda daliban Rwanda da jami’ai za su hada gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin, a fannin gudanar da ayyuka da za su gamsar da bukatun fasahohi da kasar ke da su.
Tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu, jami’ar IPRC Musanze ta yaye dalibai sama da 1,700, tana kuma gudanar da kwasa-kwasai daban daban, kamar na fasahar noman rani, da samar da magudanan ruwa, da gine-gine, da ginin manyan hanyoyi, da cinikayya ta yanar gizo, da fasahohin sadarwa.
Ya zuwa yanzu, adadin daliban jami’ar sun karu daga 171 da shekarar 2014 zuwa sama da 1,800. (Saminu Alhassan)
Source: LEADERSHIPHAUSA