Shekara 100 Da Kafa IAR: Da Sakamakon Bincikenmu Aka Kafa Ginshikin Tattalin Arzikin Arewacin Nijeriya —Farfesa Ishiyaku
A kwanan nan ne za a fara bikin cika shekara 100 da kafa Cibiyar Binciken Harkar Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Cibiyar ta bayar da gaggurumin gudumawa wajen kafa harsahin tattalin arzikin yankin Arewacin Nijeriya tun zamanin Turawan mulkin mallaka lokacin ba a kai ga gano albarkatun Man Fetur ba.
Mataimakin Editanmu Bello Hamza, ya tattauna da Shugaban Cibiyar, Farfesa Mohammed Faguji Ishiyaku a Abuja, inda ya bayyana yadda Cibiyar ta taso da yadda ta samu kanta a halin yanzu bayan cika shekara 100 tana bayar da gudumawar bunkasa harkar noma da kiwo a Nijeriya da kuma yadda ake fatan ganinta a sherkaru 100 masu zuwa. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka da kuma matsayinka
Suna na Farfesa Muhammed Faguji Isiyaku
Farfesa ita wannan cibiya tana bikin cikar shekara 100 da kafuwa, don bayani ya nuna cewa an kafa ta a ranar 4/10/1922. To yaya wannan abin yake gare ka musamman a matsayinka na shugaban wannan wuri a daidai wannan lokaci?
To wannan abin alfahari ne da farin ciki da ya kasance a lokacin shugabancinmu ne wannan cibiya tamu mai albarka ta cika har shekara 100, domin bikin cikar wannan al’amari na tarihin wannan cibiya wani babban al’amari ne wanda dukkanmu muke alfahari da shi wadda ba kowa ne Allah yake nufarsa da samun wannan ba.
Saboda haka ni a matsayina na jagoran wannan cibiya a daidai wadannan shekaru kamar yadda ka fadi abin alfahari ne a gare ni, musamman ma wanda a lokacin ne ake da bukatar hango me ya kamata a sa a gaba zuwa gaba kuma.
Wace bita za ka yi na wasu muhimman bincike da ya amfani al’umma da cibiyar nan ta yi a cikin shekara darin nan?
To da farko dai a tarihance ita wannan cibiya ta kasance cibiya ce ta dabarun noma da bincike kan dabarun noma na zamani tun lokacin mulkin mallaka, tun da an ce 1922, kowa ya san lokacin muna karkashin mulkin mallaka ne na Turawan Ingila. A wancan zamani wanna cibiya tamu ta taka rawar gani sosai, domin ta sanadin bincie-binciken masana wancan lokacin ne aka shigo mana al’amura irin su noman Gyada, da su Auduga da kayan marmari irin su Kabeji da dangin su Albasa da sauransu. Saboda mai bincke ko mai karatu zai tuna da wadansu abubuwa da suka yi karfi sosai, misalin Auduga, yadda Auduga ta zamar wa mutane musamman na Arewa kudaden shiga sosai mutane suka samu arziki mai yawan gaske, da Dalar Gyada wadda aka tuna da ita wanda a nan ne saboda ingantattun iri aka mika a hannun manomammu a wancan zamani suka noma su suka tana suka samu kudade masu dimbin yawa har ma tattalin arzkin kasar gaba daya ya bunkasa.
Amma bayan tafiyar Turawa kuma, kada in manta da shigowar bakin abinci irin su Dankalin Turawa, Mangwaro masu yi da wuri da kuma zaki da dai abubuwa da yawa. Sannan a binciken da wannan cibiya ke yi ban da amfanin gona har ma da dabbobi, su shanu da tumaki da sauransu. Amma daga baya a 1973 ko da biyar aka wafce wani bangare na binciken dabbobi shi ne ya zama cibiyar binciken inganta kiwo da dabbobi da ke Shika, to shima daga cikin IAR aka samo shi.
Wacce gudunmawa wannan cibiya ta bayar wajen samar wa al’umma abinci in aka yi la’akari da tsare-tsaren da wasu gwamnatoci suka samar, kamar irinsu shirin Operation Green Rebolution na gwamnatin Marigayi Shagari, da Back to Farm na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lokacin yana mulkin soja?
To ita cibiyarmu dama bincikenta a dunkule ya fuskanci samar da ingantattun iri, wato idan an ce iri ingantacce ne, zai zama yana da arahar nomawa, wato ba za a kashe kudi sosai ba kuma za a samu amfani mai yawa. Sannan na biyu irin rainon da za a yi masa dabaru dabaru wajen rainonsa, noma nawa za a yi masa, ban ruwa wane irin adadin ruwa za a bashi, tazarar tsakanin shuka da shuka yake, wanda duk zai nuna yadda zai habaka amfanin, maimakon in aka yi amfani da shi ta hanyar gargajiya ba tare da la’akari da sakamakon bincike ba ana iya samun buhu 10, amma idan aka bi wadannan dabaru na raino za a iya samun buhu 25 ko ma fiye da haka. Sai kuma banbancin irin ingantacce da wanda ba ingantacce ba, banbancin shi ne, iri mai inganci a Kadada daya kana iya samun kamar buhu 20, sannan na gargajiya wanda ba a inganta shi sosai ba bai wuce a samu buhu bakwai ba.
To duk wancan tsare-tsare na gwamnati da ka ambata dukkansu an dora su ne a kan samar da ingantaccen iri da kuma hanyar noma na zamani.
Tarihi ya nuna cewa an kafa cibiyar ce domin ta zamana ta taimaka wa mutanen yankin Arewa, lokacin da aka kara jihohi sai ya zamana tana karkashin Jihohin Jigawa, Kano, Sakkwato, Zamfara da Kaduna, to yaya alaka ta kasance tsakanin shekara 100 da wadannan jihohi ta hanyar amfana da wannan cibiyar bincike?
To duk da yake an kirkiro jihohi an kakkara a yadda yake a matsayin jiha guda daya Arewa ta zo ta zama jihohi 12, ta zo ta zama 19 a yanzu, saboda haka kowace jiha an kirkiro ta tana da ma’aikatar aikin gona nata na kanta, sannan kuma tana da hukumar bunkasa aikin gona a karkashinta.
To wadannan hukumomi na bunkasa aikin gona wato ADP, muna nan wannan tsohuwar dangantar da ke tsakaninmu da su na su zo su samu fasahohi na zamani a wajenmu ya ci gaba, hasali ma kowacce jiha ta kan aiko a tura mata idan ta ga wata matsala da ta sha kanta, sai su kira su sanar da cibiyarmu a tura musu masana su je su warware musu, misali a kwanan nan an samu bullar cuta a gonaki Citta a Jihar Kaduna, ma’aikatar aikin gona ta Jihar Kaduna ta tuntube mu muka tura masananmu muka je kuma masananmu suka ba wa manoman shawara da irin yadda za su shawo kan wannan ciwo, duk manoman da suka yi amfani da shawarwarin masananmu Cittarsu ta warware sai wadanda suka makara.
To kasancewar ita wannan cibiya ta riga Jami’ar Ahmadu Bello wanzuwa, to kuma a doka kuna karkashin Jami’ar Ahmadu Bello ne duk da yake akwai wasu cin gashin kai da kuke yi, ya dangantakarku da Jami’ar Ahmadu Bello?
Wannan shi ne daya daga cikin yanayi na rayuwa da ba a cika sani ba, cewa da ya haifi ubansa, kusan haka ne ya faru. A gaskiya ne domin kusan sai bayan shekara 40 da kafuwar IAR sannan aka yi Jami’ar Ahmadu Bello, to lokacin ita jami’ar ita ma ta jihohin Arewa ce, to daya daga cikin abin da ya sa aka ajiye jami’ar a inda take shi ne, kasancewar wannan cibiyar ta IAR tana nan, don an yi ittifakin cewa jami’ar nan abubuwan da za ta koyar dole har da aikin noma da aikin gona da sauransu. Saboda haka Tsangayar koyar da aikin noma da kiwo sai ya zo ya zauna a harabar IAR, sauran tsangayoyi aka yi a kusa da kwalejoji. Sai kuma batun danganta, dangantakarmu ita ce, duk wani ma’aikacin cibiyat IAR to kuma malamai ne mai koyar da karatu a Tsangayar karatu ta aikin gona, kuma duk wani malami na Tsangayae koyar da karatu na Jami’a, to shi kuma ma’aikaci ne na bincike a IAR, to wannan ita ce dangantakarmu, sai dai banbanci shi ne, albashin ma’aikatan IAR wadanda ake cewa ma’aikatan bincike, ta wajen albashi kawai ake samun banbanci, albashin ma’aikatan IAR ana dauko shi ne daga aljihun ma’aikatar aikin gona ta tarayya, sannan su kuma na Tsangayar Jami’a dungurugun ana dauko albashinsu ne daga aljihun ma’aikatar ilimi ta tarayya, amma ta wajen aiki da kuma rike mukamai duk kowa yana iya rike koowane mukami a kowane waje.
To yanzu ganin cewa wannan cibiya ta cika shekara 100, na abin da ka zo ka tarar na ayyukan da aka yi binciken da ka zo ka tarar, ina aka dosa, wane irin fata ne ake so a gani a shekaru masu zuwa?
To wannan shi ne, dama amfanin waiwaye kenan, in ka waiwaya ka ga da inda ka tabo sannan kuma zai taimaka maka wajen gano inda za ka sa gaba. To da muka zauna muka dubi abubuwan da aka yi da kuma ake cikin yi yanzu, muka yi hasashen cewa nan da shekara 100 masu zuwa, me da me muke so mu gani cewa wannan cibiya ta fuskanta.
Na farko dai muna so mu ga cewa kowane amfani da muke aiki da shi shekara 100 masu zuwa, mun ribanya shi kamar sau 10, misali, idan yanzu muna samun buhu saba’in ne a Kadada daya na masara, muna so mu bullo da ya kasance masara zai ba da buhu 700 a Kadada daya, idana ana noma dawa ta ba da buhu 20, mu samu dawa mai ba da buhu 200, ban da ma mai ba da buhu 200 nan gaba, banda ma mai 200 idan yanzu buhun taki biyar ne zai ba da wannan to yanzu muna so ya zamana taki buhu daya da rabi zai iya baka wancan amfanin.
Ma’ana muna so mu rage amfani da abubuwa kafin a samo mai yawan gaske. Sai kuma muna ta fuskantar kalubale na dumamar yanayi, muna so mu bullo da iri da kuma dabaru ta yadda manoma za su magance illolin da wannan abin yake haifarwa, kamar su ambaliyar ruwa, yawancin amfaninmu yanzu da zarar ruwa ya zo ya malale wuri in dai ruwan ya kwanta a gindinsa sati daya sati biyu to sai dai dai amfanin ya rube, to muna so mu samo dabaru na ingantattun iri da kuma dabaru na fasahar injiya na muhalli yadda ba zai hana amfani ya ci gaba ba.
Source LEADERSHIPHAUSA