Hukumomin Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Man Fetur na kasar sun sanar da cewa akwai yiwuwar maidawa dillalan kasashen ketare, gurbataccen man fetur da kamfanin man Najeriyar ya saya daga gare su.
Wannan sabon rahoto dai ya zo ne a daidai lokacin da aka shafe wasu kwanaki ana fama da layukan ababen hawa a gidajen sayar da mai, sakamakon karancinsa, abinda kai iya zama kai tsaye yana da alaka ta kai tsaye da matsalar miliyoyin litar gurbataccen man da aka gano an shigar da shi Najeriya.
Rahotanni daga hukumomin jihohi da dama a tarayyar Najeriya, cikinsu Abuja, da Legas, da Neja, da kuma Nasarawa sun ce gidajen sayar da mai sun cika makil da masu ababen hawa da sauran masu amfani da man na fetur.
Tuni dai wasu majiyoyi suka ruwaito cewar, hukumomin da abin ya shafa na kokarin shawo kan matsalar, said ai mai yiwuwa karancin man da kuma dogayen layukan ababen hawan a sassan Najeriya ka iya kaiwa zuwa karshen wannan mako.