Wednesday, December 25, 2024

Hukumar Kwastam Ta Kama Kwantena Makare Da Bindigogi A Legas

Rahotanni daga jihar Legas a tarayyar Najeriya sun ce jami’an hukumar Kwastam da ke tashar jiragen ruwa ta Tin can, sun kama wata kwantena makare da bindigogi.

Wata majiya ta shaidawa jaridar daily trust da ake wallafa ta a Najeriya cewa da fari wanda ya mallaki kwantenar ya shaidawa jami’an hukumar ta Kwastam cewar na’urorin Talabijin ne kirar zamani a ciki, to amma bayan gudanar da bincike aka gabo adadin muggan bindigogin masu yawa a ciki.

Kawo yanzu dai babau karin bayan kan yawan bindigogin da kwantenar da aka kama ta kunsa, har sai an kammala gudanar da bincike, domin bankado wanda ya mallaki makaman.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jami’an tsaron Najeriya ke kama manyan kwantenoni makare da makamai ba a tashohin jiragen ruwan kasar da ke jihar Legas, domin kuwa a watan Janairun shekarar 2017, jami’an Kwastam suka kame tarin makaman da yawansu ya kai a iya rabawa bataliyar soji.

RELATED POSTS

Adadin bindigogin da aka kama a shekarar ta 2017 dai ya kai 661 boye cikin akwatuna 46, cikin wata kwantena mai tsawon kafa 40.

Yayin da yake Karin bayani kan kamen a birnin Legas, shugaban hukumar Kwastam din Najeriyar Kanal Hamid Ali mai ritaya, ya ce a daya daga cikin kwantenonin, an yi yunkurin batar da sawun shinkafar ta hanyar lullubeta da kayayyakin gyaran ababen hawa.

Shugaban na Kwastam ya ce baya ga kwantenonin shinkafar 34, sun kuma yi nasarar kame wasu Karin kwantenonin 11, da suka hada da masu dauke da magungunan da ba’a yiwa rijista ba, tayoyin da aka yi amfani da su, tufafi da kuma man girki.

Cikin watan Satumba gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe dukkanin iyakokinta na kan tudu, domin kawo karshen matsalar fasakaurin kayayyaki da dama, ciki har da shinkafar kasashen ketare, domin bunkasa nomanta a cikin gida.

Zalika cikin watan Agustan da ya gabata, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci babban Bankin Kasar, CBN da ya dakatar da bayar da kudaden waje ga masu shigo da abinci cikin kasar domin bunkasa harkar noma a cikin gida.

Kodayake shugaba Buhari bai yi karin bayani ba, amma rahotanni na cewa, tuni babban bankin na CBN ya daina bayar da kudaden ketare ga masu shigo da shinkafa da man-ja da man-gyada da nama da ganyayyaki da kajin gona da kwai da talatalo da kifin gwangwani da tumatur da dai sauran nau’ukan abinci har guda 41.

Related Posts

Next Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED