Wani babban burin da kasashe masu tasowa suka sanya a gaba shi ne ci gaban hadin tattalin arziki, da zamanantar da kasa.
Sai dai a karkashin tsarin kasa da kasa da kasashen yamma suka kafa, abu ne mai wuya a cimma wannan buri. Abun da ya faru a janhuriyar Nijar, wani misali ne a wannan fanni.
Inda ko da yake akwai cece kuce game da tasirin juyin mulkin da aka yi, al’ummar kasar sun bayyana ra’ayinsu sarai yayin da suke zanga-zanga. Sun ce: “A kasarmu akwai ma’adinai iri-iri. Ga zinariya, da Uranium. Amma me ya sa muke ci gaba da fama da talauci? ” A ganinsu wasu manyan kasashe dake yammacin duniya ne suke da alhakin hakan, saboda babban batun da ya hana Nijar samun ci gaba shi ne tsarin kasa da kasa da su kasashen yamma suka tanada.
Sai dai ta yaya za a iya daidaita wancan tsohon tsarin? To, don cimma wannan buri, dole ne a dogara kan hadin gwiwar kasashe masu tasowa.
A wajen taron kolin tsarin BRICS da ya gudana a kwanan baya a kasar Afirka ta Kudu, dumbin kasashe masu tasowa sun nuna karfinsu sosai, inda suka cimma matsaya daya kan wasu manyan batutuwa da yawa, tare da nuna cewa, ta hanyar hadin gwiwa, kasashe masu tasowa za su iya biyan bukatun juna, da daidaita tsare-tsaren kasa da kasa, da neman samun karin ikon fada a ji a duniya, gami da tabbatar da moriyarsu ta bai daya. Kana taron tattaunawar shugabannin kasashen Afirka da kasar Sin, da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa suka jagoranta, wanda ya gudana a gefen taron kolin BRICS, ya nuna wani hali mai inganci na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, inda ake girmama juna, da rufa wa junansu baya, da nuna sahihanci, gami da neman samun hakikanin sakamako.
A wajen taron BRICS na wannan karo, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sha aiki sosai. Inda a cikin wa’adin taron na kwanaki 3, ya gana da shugabannin kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal, da Habasha, da na sauran kasashe 4 dake nahiyar Afirka.
Daga bisani a wajen taron shugabannin Afirka da na kasar Sin, shugaban ya tattauna tare da manyan shugabanni 12, da suke wakiltar kasashe, da kungiyoyin shiyyoyi, duk a nahiyar Afirka. Ta Haka, za a iya ganin yadda shugaban ke kallon kasashen Afirka da muhimmanci matuka.
Sa’an nan, idan mun yi tsokaci kan jawabin da shugaba Xi ya yi a wajen taron tattaunawar, gami da wata hadaddiyar sanarwar da mahalarta taron suka gabatar a hadin gwiwarsu, za mu san da cewa, kasashen Afirka da kasar Sin suna da bukatun iri daya, wato dukkansu na neman zamanintar da kasashensu, da wani tsarin kasa da kasa mai adalci, da zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da wani muhallin tattalin arziki na bude kofa, inda ake lura da moriyar kasashe daban daban. Hakan ya nuna tushe mai karfi na yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da kasar ta Sin.
Ban da haka, za mu iya ganin yadda kasashen Afirka da kasar Sin suke girmama juna, da kokarin rufawa junansu baya.
A wajen taron tattaunawa na shugabannin kasashen Afirka da kasar ta Sin, bangaren kasar Sin ya ce yana goyon bayan yunkurin kasashen Afirka na dunkule kansu waje guda, da mai da kungiyar AU daya daga cikin mambobin kungiyar G20. Kana kasar Sin ta yi alkawarin hada tsarinta na raya kasa, tare da na kasashen Afirka.
Yayin da a nasu bangare, dimbin shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron sun jinjinawa kasar Sin, kan yadda ta gabatar da shawarwari na tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da ci gaban al’adu a duniya, da zummar yada manufar kasancewar mabambantan bangarori masu fada a ji a duniya.
Ta la’akari da yadda aka dade ana zama a karkarshin wani tsarin kasa da kasa da kasashen yamma suka kafa, za a bukaci jan hali da basira, don nacewa kan bin wata turbar da aka zaba da kai, da kokarin neman samun nasarori, gami da samun goyon baya daga abokan hulda.
Kana wasu shirye-shirye da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a wajen taron, wadanda suka shafi yadda kasar Sin za ta taimaki kasashen Afirka raya bangarorin masana’antu, da aikin gona, da horar da ma’aikata, sun nuna takamaiman matakan da kasar Sin za ta dauka, don biyan bukatun kasashen Afirka a kokarinsu na zamanintar da kasa.
Hakan ya nuna gaskiyar huldar hadin kai da ake samu tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, inda ake lura da bukatun da ake da su, da kokarin cika alkawari, maimakon tsayawa kan kalmomin baka.
A ganin duk wata kasar dake kan hanyar tasowa, ba wani abun da ya fi damun ta, sama da yadda za a hana ta samun ci gaban tattalin arziki.
Sai dai wani albishir da muka samu shi ne, kasashe masu tasowa sun riga sun fara samun cikakken karfi, inda za su iya samar da gyare-gyare kan tsare-tsaren kasa da kasa, ta hanyar yin hadin kai a tsakaninsu.
Kana hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar ta Sin abin koyi ne a wannan fanni, ga sauran kasashe masu tasowa. (Bello Wang)
Source: LeadershipHausa