Gwamnatin Najeriya zata baiwa kowacce Jiha daga cikin Jihohin ta 36 Dala miliyan 20 domin amfani da su wajen rage radadin da annobar korona ta haifar daga cikin tallafin Dala miliyan 750 da ta karbo daga Bankin Duniya.
Ministan kasa a ma’aikatar kasafin kudi da tsare tsaren kasa Clem Agba ya bayyana shirin raba kudaden wanda yace zai fara daga ranar 30 ga wannan wata na Yuni.
Gwamnatin tace kowacce Jiha zata karbi wadannan makudan kudade ne a cikin shekaru 2, yayin da Babban birnin Tarayya na Abuja zai karbi Dala miliyan 15.
Gwamnatin tace ana bukatar amfani da wadannan kudade ne wajen rage radadin da annobar korona ta haifar ta hanyar taimakawa matalauta da masu kanana da matsakaitan masana’antu da kananan manoma.
Yau Najeriya ke bikin cika shekaru 22 da sake dawowar dimokiradiya a cikin kasar bayan juyin mulkin da soji suka yi a shekarar 1984 wanda ya katse Jamhuriya ta biyu a karkashin mulkin shugaban kasa Alh Shehu Usman Aliyu Shagari.
Olusegun Obasanjo ne shugaba na farko da ya karbi ragamar tafiyar da kasar a karkashin sabuwar Jamhuriya ta 4 a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999, inda ya kwashe shekaru 8 yana mulkin kasar bayan ya samu nasarar zabe zagaye na biyu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.
Bayan kammala mulkin shugaba Obasanjo, Yan Najeriya sun zabi Malam Umaru Musa Yar’adua a matsayin shugaban kasa a shekarar 2007 amma bayan kusan shekaru 2 sai ya rasu sakamakon rashin lafiya, abinda ya baiwa mataimakin sa Goodluck Jonathan damar karbar ragamar mulki da kuma sake zaben sa a shekarar 2011.
A shekarar 2015 an zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, kuma ya sake samun nasara a zaben shekarar 2019.
Yaya kuke kallon wannan tafiya na mulkin dimokiradiya a Najeriya?