Fadar gwamnatin Najeriya ta ce mutumin da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ICPC ke farauta kan satar dala miliyan 65 mai suna Gimba Kumo ba surikin shugaban kasar Muhammadu Buhari bane kamar yadda ake ta yayatawa.
Bayanai sun ce Gimba Kumo da ya taba rike mukamin babban daraktan bankin kula da samar da gidaje na kasa, ya auri ‘ya ga shugaban Najeriya a shekarar 2016.
Sai dai kakakin fadar shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya ce wannan alaka ta surukuta fa ta katse a shekarun baya.
Yanzu haka dai hukumar ICPC ne cigaba da neman Gimba Kumo da kuma wasu mutane biyu Tarry Rufus da ogunsola Bola ruwa a jallo, bisa tuhumarsu da yashe dala miliyan 65 daga baitulmalin gwamnati.
A wani labarin na daban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, to soma bincikar manyan jami’an hukumar raya yankin Niger Delta NDDC, kan zarge-zargen halasta kudaden haramun da kuma sace makudan kudaden da gwamnati ta ware don yakar annobar coronavirus.
An jiyo Ogugua yana fadar cewa binciken da suke a halin yanzu ya maida hankali ne kan zargin da ake wa manyan jami’an hukumar raya yankin Niger Deltan na karkatar da naira biliyan 5 da kusan rabi, da aka ware domin sayen kayayyakin baiwa ma’aikatan lafiya kariya daga cutar coronavirus, tare da tallafawa jihohi 9 wajen dakile annobar.
Kakakin hukumar yaki da laifukan rashawar ta ICPC, ya kara da cewar, sun kuma kaddamar da bincike kan batan dabon miliyoyin nairar da aka baiwa hukumar yankin Niger Deltan ta NDDC domin tura ma’aikatanta daukar horo a kasashen ketare a lokacin da annobar coronavirus ta dakatar da zirga-zirga a duniya, shirin da har yanzu ba a aiwatar ba.