Kwamitin da ke kula da asusun ajiya na kasa, FAAC ya tara Naira Tiriliyan 1.594 A Watan Satumba, ya raba Naira Biliyan 903 Zuwa bangarorin Gwamnati Uku.
Kwamitin FAAC ya sanar da samun kudaden shiga na Naira tiriliyan 1,594,763 daga watan Satumban 2023.
Wannan shi ne karo na biyu da gwamnati ke samun karin kudaden shiga tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayu.
FAAC a cikin wata sanarwa da ya fitar ta ce, ta amince da jimillar kudi naira biliyan 903.480 daga kudaden shigar da ake da su domin rabawa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
A wani labarin na daban kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa za ta yanke hukunci kan karar da ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta shigar, inda ta ke kalubalantar nasarar Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a 28 ga watan Oktoba, 2023.
Idan dai za a iya tunawa, jam’iyyar APC da ‘yar takararta ne suka shigar da kara kan ayyana Gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
APC ta yi zargin karya dokokin zabe da kuma tafka magudin zabe. APC da Binani a cikin kokensu, sun bukaci kotun ta tabbatar da sanarwar da kwamishinan zabe na jihar, Hudu Yunusa Ari ya yi wanda ya ce, APC ce ta lashe zaben.
A bangaren Jam’iyyar PDP da dan takararta, Fintiri, sun gabatar da bukatarsu a gaban kotun inda suke neman kotun da ta yi watsi da karar da APC da ‘yar takararta suka shigar.
Source LEADERSHIPHAUSA