Batun dokar mafi karancin albashi dai batu ne da ba yau aka fara shi ba, an kusan shafe shekara uku kan batun, amma har yanzu akwai jihohin da basu aiwatar ba.
Gwamnatin Tarayya ta bullo da tsarin da zai zama albashin da za’a bada mafi karanci shine N33,000 duk wata.
Ministan Kwadago da samar da aiyukan yi yace inde za’a aiwatar da tsarin dokar to za’a samu ci gaba a Nigeria sosai da sosai.
Gwamnatin tarayya tace aiwatar da tsarin biyan mafi karancin albashi abu ne da zai mutukar taimakawa sosai da sosai wajen ci gaban kasa Ake Batun Mafi Karancin, rahoton The Punch.
Wannan na kunshe ne cikin jawabin da ministan Kwadago da samar da aikin yi Dr Chris Ngige yayi a wani taron karawa juna sani kan yadda za’a kula da yadda za’a aiwatar da mafi karancin albashi, a Abuja, wanda hukumar kula da albashi da hakokokin ma’aikata ta shirya.
Ministan yace: “Tabbatar da mafi karancin labashi zai sa a ga canja a wajen ma’aikata.”
“Ma’aikacin da yake samu hakkinsa, zaka ga yadda zai rike aikinsa da muhimmanci, wannan kuma shine zai taimaka wajen tafiyar da kasa da ci gabanta ”
Akwai bukatar ayi gaggawar aiwatar da tsarin, musamman ma akan ma’aikata da kuma tabbatar da tsarin ya dore dan cin moriyarsa”
Jaridaar NNNews tace shugaban hukumar NSIWC, Ekpo Nta yace hukumar tana duk mai yiwa wajen aiwatar da tsarin, musamman ma a fannin albashi da sauran hakkoki Yace: “Hukumar nan zata tabbatar basu samu karanci ko yankewa daga aiwatar da wannan tsarin nan mafi karancin albashi ba”
Akan batun sa ido da bibiya da aka bijiro da shi shekara uku da suka shude, an yi shine dan tabbatar da yadda ake kashe kudaden ma’aikata, inji shugaban hukumar.
Wasu masu fada aji sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta sanya idanu wajen aiwatar da batun mafi karancin albashi har ma da sauran bukatun ma’aikata, kamar yadda su ka ce wasu hukumomin gwamnatin basa bin dokokin hukumar.
Kudirin dokar aiwatar da tsarin mafi karancin albashi dai ba sabon abu bane, tun shekarar 2019 gwamnati ke kokarin aiwatar dashi.
Duk da akwai jihohin da suka aiwatar kamar Jigawa, Kano da Kaduna, amma har yanzu akwai ma’aikatun gwamnatin tarayya da basu aiwatar ba.
Source:LegitHausa