A ƙarshe, Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya yi ƙarin haske kan ziyarar da jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu’annati (EFCC) suka kai babbar hedikwatar kamfanin na baya-bayan nan, kuma ya ba da tabbacin cewa, kamfanin zai taimaka wa hukumar wajen gudanar da bincike.
Jami’an EFCC sun ziyarci hedikwatar rukunin Dangote ne da ke Legas kan bayanan kuɗaɗen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ware mata daga shekarar 2014 zuwa yanzu.
Kwanaki bayan ziyarar, Dangote a wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya bayyana cewa, “Kamar yadda aka yi ta yaɗa rahotannin ziyarar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi zuwa babban ofishin mu da ke Jihar Legas a ranar 4 ga watan Janairun 2024, mun fahimci irin karsashin da abokan hulɗar mu da kuma sauran al’umma su ke da shi domin sanin haƙiƙanin abin da ya faru, hakan ne ya sa za mu sanar da ku haƙiƙanin abin da ya faru.
“A ranar 6 ga watan Disamba, 2023 mun samu wasiƙa daga Hukumar EFCC, inda ta bukacibmu ba su ba’asin kuɗaɗen waje (Dalar Amurka) da CBN ya ba mu daga shekara 2014 zuwa yanzu.
Mun fahimci cewa ba mu kaɗai aka baiwa wannan wasiƙar ba, an turawa wasu kamfanonin kimanin 51 irin wannan wasiƙar kuma suma ana neman wannan bayanin daga gare su,” inji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mun baiwa Hukumar EFCC takardar karɓar buƙatar da suka turo mana, muka kuma buƙaci su yi mana ƙarin bayani a ɓangaren da suke buƙatar bayani, ko kuma daga wane ɓangare na rukunin kamfanonin mu.
Mun kuma buƙaci ƙarin lokaci domin haɗawa tare da gabatar musu takardun da suka kai shekaru goma.
“Duk da cewa, hukumar EFCC ba su fayyace mana ɓangaren da suke da buƙatar bayanan ba, kuma ba su bamu damar da muka buƙata daga gare su ba dangane da ƙarin lokaci, suka kafe akan lallai suna da buƙatar wannan bayanai a ƙurarren lokaci, amma mun tabbatarwa hukumar EFCC cewa za mu gabatar musu da bayanan da suka buƙata a lokuta daban-daban saboda muna kan kammala tattara bayanan.”
Sanarwar ta cigaba da cewa, “A ranar 4 ga watan Janairu 2024, ma’aikatan mu suka fara miƙawa Hukumar EFCC rahoto kashi na farko.
Baya ga haka, jami’an hukumar EFCC suka ƙi karɓar takardun rahoton da muka gabatar musu, suka ƙi amincewa da kai musu da aka yi, suka nace akan dai su zo ofishin mu su karɓi wannan kwafin rahoton da muka gabatar musu da kansu.
“Duk da kasancewar ma’aikatan mu suna ofishin su da takardun bayanan da suka buƙata, wasu daga cikin jami’ansu suka wuce zuwa ofishin domin karɓar wannan rahoton da aka gabatar musu wanda hakan ya zubar mana da kima da kuma taɓa darajar mu.
Bugu da kari, jami’an nasu ba su ɗauki wasu takardu ko kuma wani kundi daga ofishinmu ba a yayin da suka kawo ziyarar ofishinmu ba, domin duk abinda suke nema yana ofishinsu.
“Muna faɗa da babbar murya cewa, babu wani zargi ko kuma wata badaƙala da ake zargin ɗaya daga cikin rukunin kamfaninnikan lmu da ita a wannan lokacin, face dai muna bayar da bayanan da aka buƙata daga gare mu domin taimakawa hukumar EFCC a binciken da ta ke yi.
“A matsayinmu na kamfanin da ya ke biyayya ga dokokin ƙasa, a shirye muke da mu ba da haɗin kai wajen bai wa hukumar EFCC duk wani bayani da suke da buƙata daga wajen mu.
Mun riga mun miƙa musu kason farko na bayanan da suka buƙata daga gare mu, muna kuma aiki tuƙuru domin ganin mun ba su sauran bayanan da suka rage daga gare mu akan lokaci, domin taimakawa binciken da suke yi.
“Gamayyar Kamfanonin mu suna daga cikin waɗanda suka fi bada gudunmawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasar nan, kuma ɗaya cikin manyan kamfanonin da ke kasuwar hannayen jarin ƙasar nan, sannan kuma ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da suka fi biyan haraji mai yawa a ƙasar nan. Mun kasance masu biyayya ga dokokin ƙasa tare da kare martabar ta a yunƙurin da Gwamnatin Tarayya ta ke yi na ganin an samar da bunƙasar tattalin arziki ta yadda masu zuba hannayen jari na gida da na waje za su samu damar yin hakan”, inji sanarwar.
A ƙarshe, sanarwar ta ce, “Muna kira ga abokan hulɗarmu su fahimci yadda abin yake, su kuma kwantar da hankulansu. Za mu ci gaba da sanar da su duk halin da ake ciki lokaci-zuwa-lokaci.”
Source: LEADERSHIPHAUSA