Cibiyar binciken harkar noma ta Jami’ar Ahamadu Bello da ke Zariya (IAR), ta yi taron gani da ido na fitar da Irin Masara mafi inganci ga manoman wannan kasa baki-daya.
Daya daga cikin wadanda suka jagoraci wannan bincike, Farfesa Rabi’u ya bayyana cibiyar binciken harhar nomar wato, ‘Institute of Agriculture Research’ a matsayin wadda ta fitar da ranar 12 ga watan Satumbar shekarar 2023, domin shaida wa duniya shirinta na ‘TELA MAIZE’, ma’ana rana ta musamman don nuna wa kasarmu da manoman duniya Irin Masara mai suna ‘TELA’, wacce take dauke da sinadarai masu yawan gaske.
Ya ce, dalilin gudanar da wannan taro a wannan gona shi ne, domin manoma su shaida banbancin da ke tsakanin sabon Irin ‘TELA MAIZE’, da kuma saura Irin da ake da su a halin yanzu.
Farfesan ya kara da cewa, a wannan gona ana shuka masara kala daban-daban, don tantance abin da cibiyar ke son jama’a su shaida tsakanin sauran Irin masarar da sabo na ‘TELA MAIZE’.
A kalla manoma daga cibiyoyi da kungiyoyi daban-daban sun gamsu da wannan sabon Iri da wannan cibiya ta kirkiro a zamanace tare da yin jinjina ga wannan nazari na bincike da aka gudanar.
Shi ma a nasa tsokacin, Shugaban Cibiyar Farfesa M.F Ishiyaku, ya ce, “Da farko ina godiya a madadin ‘Institute for Agricultural Research’ ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya, wadda ke jin dadin kula da daukar nauyi daga Ma’aikatan Aikin Gona ta tarayya, ina yi muku barka da zuwa wannan hamshakin taro na gani da ido. Ina kuma mika godiyata ta musamman, ga manoma, musamman wadanda suka tari aradu da ka suke karbar fasahohinmu na gwaji, domin tarar aradu da ka ne ka karbi abin da ba ka san ingancinsa ba, saboda ka ba da gaskiya ka jarraba shi, domin ta hanyar ka wani dan’uwanka ma zai gani ya assasa wannan abin, shi ya sa har kullum bincikenmu ba ya cika har sai mun shigo da manoma ciki sun sa mana hannu kafin ya samu karbuwa.”
Saboda haka, ya kamata manoma mu fahimta cewa wannan daya daga cikin yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi na rage matsalolin noma a wannan kasa. Daya daga cikin matsalar da manomi ke fuskanta ita ce, matsalar hauhawar farashi ta yadda zai zuba jari a harkarsa ta noma har ya ci riba.
Sa’annan, shugaban kungiyar binciken ya yi bayani dangane da yadda wata tsutsa da ake kira da cema ‘Fall Army Worm’, wadda manoman masara a ‘yan shekarun nan muka wayi gari Allah ya jefo mana ita, wanda idan ba a yi sa’a ba sai kaa wayi gari ka ga gonarka da take da yabanya mai kyau, ana sa rai za a samu abin kirki sai ka ga duk daga zuciyarta ta lalace an yi asarar ta baki-daya.
Har ila yau, babban makasudin wannan taro shi ne, tabbatar wa manoma cewa, tana iya yiwuwa a bullo da ingantaccen Iri na masara, wanda zai jure kansa ba tare da an yi masa feshin
magani ba, ma’ana zai iya jure kansa da kansa. Mun gamsu wannan sabon Iri yana da wannan inganci kwarai da gaske, amma mun zo ne domin mu sake jaddada wannan.
Saboda haka, na ke kara jinjina wa manoman da suka yi fice wajen rungumar sababbin fasahohi ba wannan kawai ba, har ma sauran fasahohi na shekarun baya da muka yi ta yi. Idan za ku iya tunawa, wannan cibiya tamu a wannan shekare ne ta cika shekaru dari da daya cif.
A wannan zamani na wannan cibiya tamu, mu muka dauki alhakin yada dukkannin wani ingantaccen aikin noma, kama daga rainon ‘ya’yan itatuwa, hatsi, dawa, gero, masara, wake, waken suya da sauran makamantansu har ya zuwa yanzu din nan, kafin a da aka yi garambawul ga irin nauye-nauyen da aka dora mana a sanadiyar sake kirkiro da wasu cibiyoyin binciken aka dan rage mana nauyi.
Akwai wadanda babu abin da ya hada su da noma, amma ganin irin fa’idar da ake samu a cikinsa ya sa suka yi cincirindo sukau rngume shi, saboda haka ina ga mu wadanda muka gaje shi a matsayin sana’a. Babu shakka, noma yana ba wa ‘yan Nijeriya kusan kashi 66 cikin 100, wanda ya yi daidai da kimanin kusan mutum miliyan 160 aikin yi.
Saboda haka, duk wani manomid a ya samu karuwar tattalin arziki, daidai ya ke da kamar ka dauki wani ma’aikaci aiki ka rika biyan sa albashi duk shekara.
Source LEADERSHIPHAUSA