Babban bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da matakin haramta hada-hadar kudi a asusun ajiyar banki da babu BVN da lambar NIN daga watan Maris din 2024.
A wata takardar da aka raba wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kudi da masu gudanar da hada-hadar kudi, Babban bankin ya ce za a hana amfani da asusun ajiyar.
Babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne asusu ya zamana yana da BVN ko NIN.
Babban bankin ya ce nan ba da dadewa ba za a gudanar da cikakken bincike kan asusun da babu BVN ko NIN, kuma da zarar an samu babu za a dakatar da asusun.
“Dukkan cibiyoyin hada-hadar kudi da Babban banki ke jagoranta ana bukatar su yi aiki da tsauraran matakai kan takunkumi kan asusun ajiya,” in ji Efobi da Mustapha a cikin takardar sanarwar.
Babban bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da matakin haramta hada-hadar kudi a asusun ajiyar banki da babu BVN da lambar NIN daga watan Maris din 2024.
A wata takardar da aka raba wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin kudi da masu gudanar da hada-hadar kudi, CBN ya ce za a hana amfani da asusun ajiyar.
Babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne asusu ya zamana yana da BVN ko NIN.
CBN ya ce nan ba da dadewa ba za a gudanar da cikakken bincike kan asusun da babu BVN ko NIN, kuma da zarar an samu babu za a dakatar da asusun.
“Dukkan cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke jagoranta ana bukatar su yi aiki da tsauraran matakai kan takunkumi kan asusun ajiya,” in ji Efobi da Mustapha a cikin takardar sanarwar.
Source: https://hausa.leadership.ng/cbn-zai-haramta-harkokin-kudi-a-asusun-bankin-da-babu-bvn-da-nin-a-2024/