Bincike ya nuna Bankin CBN zai lalata takardun kudi na kimanin N6, 000, 000, 000, 000 a cikin shekaru kusan takwas.
Babban bankin kasar yana bata duk kudin da suka tsufa ko suka yi rashin kyawun gani, sai a sake buga wasu sababbi .
Kudin da aka kashe domin ayi waje da wadannan Tiriliyoyin kudi daga yawo a hannun jama’a sun kusa kai N4bn FCT, Abuja.’
Ana sa ran babban bankin CBN na kasa zai lalata kudin da darajarsu ta haura Naira Tiriliyan shida a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Binciken da Punch ta gudanar, ya nuna zuwa lokacin da Muhammadu Buhari, bankin CBN ya dagargaza takardun wadannan kudi da suka tsufa.
Bayanan da aka samu daga ofishin sashen ayyuka na babban bankin Najeriya ya nuna daga 2016 zuwa 2020, CBN ya dagargaza Naira Tiriliyan 4.1.
A tsawon shekarun nan biyar, an lalata wadannan takardun kudi da sun yi tsufa ko sun yi lalacewar da ba za a iya cigaba da amfani da su a Najeriya ba.
Jaridar tace ba ta da bayanan adadin kudin da aka lalata tsakanin shekarar 2021 zuwa yanzu.
Amma bankin kasar ya bada sanarwar lalata 80% na Naira tiriliyan 3.2 da ke yawo. Wannan karo kudin za su tashi aiki ne saboda za a buga sababbi.
Tsakanin shekarar 2016 da 2020, alkaluman CBN sun nuna an lalata Naira biliyan 829.94 wadanda suka gurbace a dalilin kecewa ko makamancin haka.
A shekarar 2017 kuwa, Naira biliyan 977.23 aka lalata a babban bankin Najeriya na CBN.
A shekarun da suka biyo baya, adadin sun ragu; Naira biliyan 814.59 aka lalata a shekarar 2018, sai kuma aka dagargaza Naira biliyan 814.44bn a 2019.
Jaridar tace a shekarar 2021 da ta biyo baya, takardar kudin Naira biliyan 698.59 aka lalata.
Wannan ya sa aka bar jimillar adadin kan Naira Tiriliyan uku.
An kashe N3.88bn saboda a lalalta N3tr Daga 2016 zuwa 2020, kudin da CBN ya kashe domin ya lalata wadannan kudi ya zarce Naira biliyan 3.8. Ana ware kudi masu yawo domin wannan aiki.
A 2016 an batar da N1.43bn, sai N594.6m, N662.2m, N647.8m da N538.5m a shekarun da suka biyo baya na 2017, 2018, 2019 da 2020 domin a lalata kudin.
Source:legithausang