Babban Bankin Najeriya (CBN) na ci gaba da duba hanyoyin habaka amfani da kudaden zamani sabanin takardun da aka saba dasu.
Sabon kudurin bankin CBN na rage yaduwar kudade a hannun jama’a zai fara aiki ne a watan Janairun 2023, zai kuma ba da damammaki da yawa.
Bayanai da aka samo daga cibiyar NIBSS sun nuna cewa, a cikin watanni 11 na 2022, ‘yan Najeriya sun yi hada-hadar kudade N345.04tr.
Daga ranar 9 ga watan Janairun 2023, Babban Bankin Najeriya (CBN) zai tabbatar da dokarsa a kan injunan ATM, POS da sauran hanyoyin cire kudi a kasar nan.
Manufar CBN ba komai bane face rage adadin kudaden da ke yaduwa a hannun jama’a tare da daura ‘yan kasar a turbar amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani.
Babban bankin na son ganin ‘yan Najeriya na amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani ta yanar gizo ko sabanin haka a madadin tsabar kudi jingim a hannu.
Hanyoyin da ake son amfani dasu sun hada da yanar gizo, USSD, POS, manhajojin waya, ATM da dai saransu.
Yadda ‘yan Najeriya suka yi amfani da sabbin hanyoyin biyan kudi a 2022 Bayanan da aka samo daga cibiyar hadakar bankuna ta NIBSS sun nuna cewa, ‘yan Najeriya sun yi amfani da hanyoyin zamani wajen kashe kudaden da suka kai tiriliyan 345.04 a watanni 11 na 2022.
NIBSS ce ta kula da dukkan hada-hadar da aka yi ta hanyar biyan nan take (NIP) da suka da; biya ta intanet, wayan hannu, ATM, POS da USSD.
Tsarin NIP dai wani tsari ne da ake amfani dashi wajen biyan kudi nan take ga lambar asusun banki, an fara amfani da NIP a 2011, NIBSS ce ta samar dashi.
Adadin kudaden da aka yi hada-hada ta yanar gizo POS- N7.56trn
Wayoyin hannu- N16.9trn
Adadin kudaden da aka yi hada-hada ta wasu hanyoyin zamani POS – N1.06bn
Wayoyin hannu – N609.4bn
Takardun ceki -3.72m Tsarin NIP – 4.57bn Biya ta yanar gizo – 8.4m
Idan baku manta ba, na daga tsarin CBN kirkirar sabon kudi, amma hakan ya zo da tsaiko, domin an fara buga na bogi a kasar nan.
Rahoton da muka hada ya bayyana yadda za ku bambance kudin bogi da na gaske.
Source:LegitHausa