A ranar Laraba 8 Faburairu, 2023 kotun koli ta yi watsi da wa’adin 10 ga watan nan da CBN ya sanya ga ‘yan Najeriya don daina amfani da tsoffin kudin kasar; N200, N500 da N1000.
Wasu ‘yan Najeriya sun shiga farin ciki tare da tunanin matsalarsu ta kau, wasu kuma sun bayyana fushinsu game da hakan, rahoton Punch.
A tun farko, CBN ya tsawaita wa’adin 31 ga watan Janairu na daina amfani da tsoffin kudi zuwa 10 ga watan Faburairun bana.
‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar kuncin rashin sabbin Naira a bankuna da wurin masu musayar kudi na POS, wasu kuwa na siyan tsabar kudi a hannun jama’a kan wani farashi mai ban dariya da ban mamaki.
Halin da ‘yan Najeriya ke ciki Bayan duba ga wannan lamari, tuni aka fara cece-kuce tare da neman mafita, kungiyoyin fararen hula da ‘yan siyasa sun bayyana ra’ayoyinsu kan karancin sabbin kudi.
Sai kwastam, kotun koli ta ce ta tsawaita wa’adin da CBN ya bayar a wani hukunci da ta yanke.
To amma, meye hukuncin ke nufi? Ga kadan daga abubuwan da ya kamata ku sani game da hukuncin: 1. Gwamnonin APC ne suka kai karar Buhari da CBN gaban kotu Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, Yahaya Bello na Kohi da Bello Matawalle na Zamfara ne suka maka gwamnatin tarayya da CBN a kotu tare da neman a kara wa’adin daina amfani da tsoffin kudi.
Dama tun farko El-Rufai ya nuna rashin gamsuwa da wa’adin da CBN ya sanya, har yace gwamnonin APC sun gana da Buhari a kai.
2. Tsawaita wa’adin na wucin gadi ne, ba hani ne kai tsaye ga wa’adin daina karbar tsoffin kudi ba Kotun kolin ta ba CBN da gwamnatin tarayya ne da su dakatar da batun wa’adin daina amfani da tsoffin kudi zuwa wani lokaci, sabanin yadda a baya CBN ya bayar – 10 ga watan Faburairu.
Yana da kyau ‘yan Najeriya su fahimta cewa, tsawaita wa’adin da kotun ya bayar yana nufin na wucin gadi ne har zuwa lokacin da kotun za ta sake sauraran musabbin karar da gwamnonin na APC suka shigar.
3. Za sake sauraran karar a ranar 15 ga watan Faburairu Ba a san dai me zai faru ba a lokacin da kotun za ta sake zama a ranar 15 ga watan Faburairu kan batun tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin kudaden ba.
Yayin da ‘yan Najeriya za su samu saukin ci gaba da shigar da tsoffin kudade kasancewar an matsar da lokacin daga 10 ga watan Faburairu, abin da zai biyo baya a ranar 15 ga watan Faburairun ne zai zama sakamakon dindindin ga lamarin daina amfani da tsoffin kudin.
Bayan hukuncin kotun na yau ne aka samu wasu ‘yan Najeriya da suka fito domin nuna adawa da hukuncin tare da kira ga Buhari da ya tabbatar da ka’idar CBN na 10 ga Faburairu.
Source:LegitHausa