Sabon gwamnan babban bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa tsarin samar da kudade ne ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.
Sabon gwamnan ya kuma bayyana cewa, zai yi fatali da wasu tsare-tsaren magabacinsa, Godwin Emefiele, sannan zai mayar da hankali kan tsare-tsaren samar da kudade don karfafa darajar Naira.
Cardoso ya bayyana haka ne a yayin tantance shi tare da tabbatar da shi a matsayin gwamnan CBN a ranar Talata.
Mataimakan gwamnan da aka tantance kuma aka tabbatar da su, sun hada da: Emem Usoro, Abdullahi Dattijo, Bala Bello da Philip Ikeazor.
Yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan majalisar, Cardoso ya ce, babban bankin na fuskantar kalubale da dama wanda da shi da mataimakansa suka gano kuma da yardar Allah za su shawo kan matsalolin a kuma magance su.
A wani labarin na daban shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Dakta Jamila Bio Ibrahim a matsayin ministan kula da harkokin Matasa.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale da ya fitar a ranar Lahadi, shugaban ya kuma amince da nadin Ayodele Olawande a matsayin karamin ministan harkokin matasa.
Dakta Jamila Bio Ibrahim matashiyar likita ce wacce a baya-bayan nan ta kasance shugabar kungiyar Mata ta ‘Progressive Young Women Forum’ (PYWF).
Ta taba yin aiki a matsayin babbar mai taimaka wa gwamnan jihar Kwara kan manufofin cigaba mai daurewa (SDGs).
Shi kuma, Ayodele Olawande kwararren masani ne a bangaren cigaban al’umma kuma shugaban matasa ne a jam’iyyar APC.
Aikin da ya yi a baya-bayan nan kafin wannan nadin shi ne ya kasance babban mashawarci ga shugaban kasa kan kirkire-kirkiren zamani daga shekarar 2019 zuwa 2023.
A kan hakan, shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci wadanda aka nadan da su yi amfani da azamarsu, kokarinsu, hikimarsu, dabararsu wajen kyautata al’amuran Matasan Nijeriya yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Source: LEADERSHIPHAUSA