Buhari Ya Bukace EU Ta Dorawa Shuwagabannin Juyin Mulki Takunkuman Tattalin Arziki.
Shugaban Mohammadu Buhari na tarayyar Najeriya wanda ya halarci taron kwanaki biyu na kungiyoyin kasashen Afirka AU da kuma ta kasashen Turai EU a birnin Brussels, ya bukaci EU ta marawa kungiyar AU baya kan shirinta na fada da shugabanci ba irin na Democradiyya ba, wadanda suka fara kunno kai a nahiyar Afirka a shekarar da ta gabata.
Banda haka shugaban ya bukaci a tumbuke tushen ayyukan ta’addanci a nahiyar ta Afirka, sannan a magance tashe-tashen hankula ta kabilanci ko na addinin ko na bangaranci a nahiyar .
Garba Shehu babban mai bawa shugaban kasa shawara kan al-amura na musamman wadanda suka hada da kafafen watsa labarai da kuma hulda da jama’a ya ce shugaban, ya bukaci kungiyar kasashen Turai EU ta cika alkawulanda ta yi wa kasashen Afirka, ta maida alkawulan daga takarda zuwa aiki.