Gwamnan Babban bankin Najeriya CBN ya canza manyan takardun kudin Najeriya da nufin ceto tattalin arzikin kasa.
Amma bankin Duniya yana ganin a karshe tsarin zai fi yi wa tattalin arzikin na Najeriya illa ne Masana sun ce kananan ‘yan kasuwa da mutanen da suke bukatar kudi a kai-a kai za su sha wahala.
Bankin Duniya ya yi gargadi a game da canjin wasu manyan takardun kudi da babban bankin Najeriya watau CBN ya yi a kwanan nan.
Bankin Duniyan ya nuna tasirin tattalin arzikin wannan sabon tsari zai fi shafar talakawan Najeriya. Punch ta fitar da wannan rahoto a makon nan.
Wannan banki da ke birnin Washington a kasar Amurka ya fitar da rahoto na musamman wanda ya yi wa take da “Nigeria Development Update.”
A watan da ya gabata ne Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya fitar da sababbin N1000, N5000 da N200 da za a koma amfani da su a maimakon na da.
Babban bankin Najeriya yana ganin canjin kudin zai yaki matsalar garkuwa da mutane, ta’addanci, boye kudi a gidaje, da buga kudin jabu.
Ba a nan ta ke ba – Bankin Duniya Amma a ra’ayin masanan bankin Duniya, canjin kudin zai yi mummunan tasiri a kan masu kananan kasuwancin da suke bukatar kudin da za su rike.
Rahoton bankin na Duniya ya nuna buga sabon kudi ba bakon abu ba ne, an saba yi a duk kasashe, don haka babu laifi canza kudin Najeriya da suka dade.
Sai dai inda matsalar take a Najeriya, bankin CBN ya bada gajeran wa’adi domin a gama canza duka tsofaffin kudin da ake da su, hakan zai taba talakawa.
Masana suna ganin canza kudi a gurguje zai taba kananan ‘yan kasuwa da mutanen da ba su da karfi – wadanda sun dogara da kudin da za a samu kullum.
A halin yanzu, wannan banki ya ce gidaje da kamfanoni da yawa su na fuskantar wahalar tashin farashin kaya, tsananin tsadar rayuwar da ambaliyar ruwa.
Masu ruwa da tsaki sun koka Shugaban kungiyar masu amfani da banki, Dr. Uju Ogunbunka ya ce babu abin suka a game da tsarin takaita yawo da kudi illa wa’adin da CBN su ka bada.
Shi ma shugaban masu kananan kasuwanci a jihar Legas, Dr. Adebayo Adams yana ganin tsarin da bankin CBN ya fito da shi, zai taba abokan aikinsa.
Babu ruwanmu da Hon. Kazaure –
Majalisa An ji labari Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ce ikirarin da ‘Dan majalisar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi yake yi a kwanakin nan, ba da yawunsu ba.
Shugaban Majalisar wakilan tarayya ya yi wa manema labarai bayanin matsayarsu a kan zargin Gudaji Kazaure na satar N89tr daga babban bankin CBN.