Sanata Anyim Pius Anyim, wanda ke neman shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar adawa ta PDP ya bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta farka daga baccin da take yi don daukar matakai a kan rashin tsaro da ke barazanar ruguza kasar.
Ya ce matakai masu tsauri da ya kamata a dauka wajen warware matsalar tsaro sun hada da matakan soji na bai daya a wuraren da kalubalen tsaron suka fi kamari; bunkasa ababen more rayuwa a yankunan karkara akalla a cibiyoyin da ake kaddamar a yakin, da kuma bullo da shirin afuwa ga ‘yan bindiga da suka yi tuba ta gaskiya, tare da shirin samar wa da matasa ayyukan yi a fadin kasar.
Cif Anyim ya bayyana tasirin rauni da ake da shi wajen tafiyar da tattalin arzikin kasar, da kuma rashin takamamen manufofi na tattalin arziki, gami da rashin yanayi mai kyau na gudanar da kasuwanci da sauran san’o’i a matsayin matsalolin da suka ta’azzara rashin tsaro a Najeriya.
Ya bayyana dimbim guraben ayyukan yi da aka rasa sakamakon rufe masakun Kaduna da na Bompai a Kano da sauran wurare a matsayin ummul’aba’isin halin rashin tsaro da kasar ta shiga.
Anyim ya ce ko da yake lokaci yana kure wa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, duk da haka tana iya yunkurawa wajen ganin cewa sunanta bai shiga tarihi a matsayin gwamnatin da ta gaza gaba daya wajen jan akalar kasar ba.