EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta samu kudi a hannun AGF Idris Ahmed.
Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ya yi bayanin irin cigaban da suka samu a shekarar nan Kawo yanzu, Abdulrasheed Bawa ya ce jami’an EFCC sun iya karbo N30bn daga hannun tsohon AGF.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya ce zuwa yanzu an karbe N30bn daga hannun Idris Ahmed.
Vanguard ta ce wadannan biliyoyi su na cikin N109bn da ake zargin AGF Idris Ahmed ya karkatar a lokacin yana rike da ofishin Akanta Janar na kasa.
Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaidawa Duniya wannan a lokacin da ya halarci wani taro da aka yi da manema labarai dazu.
EFCC ba tayi cikakken bayani a kan kudin da aka karbe a hannun Idris ba. Tuni tuni Ministar tattalin arziki ta dakatar da shi domin a iya binciken sa.
Kwamitin harkokin yada labarai na fadar shugaban kasa ta shirya wannan zama a Aso Villa a Abuja kamar yadda aka saba lokaci bayan lokaci.
An karbe biliyoyi a shekarar 2022 Kamar yadda Abdulrasheed Bawa ya yi bayani, daga watan Junairu zuwa Disamban 2022, sun karbe N134,33,759,574.25, $121,769,076.30, da £21,020.00.
A tsakanin wannan lokaci, hukumar tayi nasarar karbe €156,925.00, ¥21,350.00, da CFA300,000.00.
Wannan bayanin yana shafin EFCC da ke Twitter
Bawa ya ce sun daure mutane fiye da 3, 615 a shekarar nan, wanda hakan ya nuna da gaske ake yi wajen yakar masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annuti.
Gwanjon motoci da SCMUL Punch ta ce a jawabin da ya yi, Bawa ya shaida cewa za a bi doka da ka’ida wajen yin gwanjon wasu motoci da aka karbe daga hannun marasa gaskiya.
Kungiya Bayan an yi gwanjon wadannan abubuwan hawa, akwai gidajen 150 da EFCC za ta sa a kasuwa, za a saida su ga mutanen da suka nuna sha’awar saye.
Wani albishir da shugaban na EFCC ya yi shi ne, da zarar sashen SCMUL ya fara aiki gadan-gadan, zai yi wahala wani mutum ya iya satar kudi a Najeriya.
SCMUL wani sashe ne na musamman da aka kirkiro da nufin yakar masu safar kudi ta haramtaciyyar hanya. An fito da wannan tsari a shekarar 2011.