Ma’aikatar Lafiya a Afrika ta kudu ta sanar da shirin fara bai wa kananan yara ‘yan shekaru 12 allurar rigakafin covid-19 a mako mai zuwa baya kokarin fara baiwa masu raunin garkuwa jiki rigakafin a karo na 3.
Ministan lafiya Joe Phaahla ya shaidawa taron manema labarai yau juma’a cewa Afrika ta kudu ta kammala shirin fara yiwa kananun yaran ‘yan shekaru 12 zuwa 17 rigakafin daga mako mai zuwa.
Karkashin dokar yaki da corona ta Afrika ta kudu dai duk yaran da shekarunsu ya fara daga 12 zuwa sama baya bukatar sahalewar iyaye kafin karbar rigakafin cutar ta covid-19.
A wani labarin na daban Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce wasu mutane ne suka kitsa tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin mutuwar mutane fiye da 212 a kasar a cikin mako guda.
Cyril Ramaphosa ya ce abubuwan da suka faru biyo bayan daure tsohon shugaban Afirka ta Kudun shiryasu aka yi inda ya kara da cewar tuni hukumomi suka gano wasu dake cikin gungun da suka tayar da fitinar da ta lakume rayukan mutane sama da 200 a kasar.
A halin da ake ciki Jami’an tsaron Afirka ta Kudu sun kame mutane sama da 500.