Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwar da ta ratsa kasar Philippines ya zarce 200, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin jinkai da kuma neman sauran wadanda suka tsira da ran su.
Rahotanni sun ce mahaukaciyar guguwar ta yaye rufin gidaje da tumbuke bishiyoyi da turakun lantarki da na sadarwa da ragargaza gidajen da akayi da katako da share gonaki da kuma haifar da ambaliyar da ta mamaye gidajen jama’a a kauyuka, abinda ya sa ake danganta da irin wadda aka gani a shekarar 2013.
Rundunar ‘Yan Sandan kasar tace ya zuwa wannan lokaci an samu gawarwakin mutane 208, yayin da mutane 52 suka bata, kana wasu daruruwa sun samu raunuka daban daban a yankin kudu da kuma tsakiyar kasar.
Adadin mutane sama da dubu 300 suka gudu daga gidajen su da yankunan bakin teku kafin guguwar ta afka musu, abinda ake ganin ya takaita illar da ta yi.
Shugaban kasa Rodrigo Duterte ya ziyarci wasu daga cikin yankunan da aka samu hadarin, inda ya bada Dala miliyan 40 domin aikin jinkai.
Tuni gwamnati ta tura sojoji da ‘yan sanda da jami’an dake gadin bakin teku da kuma masu aikin kashe gobara domin taimakawa wadanda hadarin ya ritsa da su.