Abdulsamad Rabi’u Ya Sha Gaban Mike Adenuga A Matsayin Mutum Na Biyu Mafi Dukiya.
A Najeriya Bayan Samun N87bn Cikin Awanni
A halin yanzu Najeriya ta samu sabon lamba na biyu a jerin biloniyoyi kuma shine Abdulsamad Rabiu Rabiu ya doke dan kasuwan bangaren sadarwa.
Mike Adenuga ya zama na biyu bayan hannun jarinsu sun karu da N87bn cikin awanni.
Har yanzu Aliko Dangote shine mutum mafi kudi a Najeriya, kuma shine kadai aka ambaci sunansa cikin attajiran duniya mafi yawan dukiya guda 400 Abdulsamad Rabiu, wanda ya kafa kamfanin BUA kuma shugabanta, yanzu shine mutum na biyu da ya fi yawan kudi a Najeriya.
Ya shiga wannan matakin ne a ranar Juma’a da dare yayin da arzikinsa ya karu daga $5.3 biliyan zuwa $5.5 biliyan.
Yadda Adenuga ya rikito zuwa na uku A bangare guda kuma, Mike Adenuga yana ta fama a 2022 kuma bayanai daga Forbes sun nuna dukiyarsa ta ragu da fiye da $1 biliyan.
A farkon shekarar Adenuga yana da $6.6 biliyan. Shine mutum na uku mafi kudi a Najeriya kuma na 433 a duniya.
Arzikin Aliko Dangote ya ragu zuwa dala biliyan 19, wanda yanzu ya zama na 80 mafi arziki a duniya.
A wani rahoton daban, Aliko Dangote, wanda ya kafa kamfanin Dangote kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyan Afirka, ya ga an daidaita kiyasin dukiyarsa yayin da ake sayar da hannun jari a Simintin Dangote, Rahoton Legit.NG.
A lokacin da aka kammala zaman ciniki na ranar Talata, arzikin dan kasuwar dan asalin jihar Kano ya dawo dala biliyan $19, wanda ya mayar da shi 80 a cikin jerin attajiran duniya da kididdigar Bloomberg ta fitar.
A cewar kididdigar Bloomberg, wacce ta fitar da sunayen attajiran duniya 500, yanzu dukiyar sa ta ragu zuwa dala biliyan 19 sabanin dala biliyan 20 a watan Mayun 2022.
Source:legithausang