Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta fara neman Yahaya Bello ruwa a jallo kan zargin almundahanar Naira biliyan 80.2.
EFCC ta yi kira ga duk wanda ke da bayanan da za su kai ga cafke tsohon gwamnan Kogi, ya kai rahoto ga hukumar ko ‘yansanda.
Wannan na cikin wani sakon da hukumar ta wallafa a yammacin ranar Alhamis a shafinta na Facebook.
“EFCC na neman tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin badakalar Naira biliyan 80.2,” in ji EFCC.
“Duk wanda ke da bayanin inda za a same shi, ya kamata ya kai rahoto ga EFCC ko ofishin ‘yansanda mafi kusa da shi.”
A wani labarin na daban shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje da matarsa da dansa ba su halarci zaman babbar kotun jihar Kano ba a ranar Larabar nan domin amsa tuhumar da ake yi musu na cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudaden gwamnati.
In ba a manta ba, LEADERSHIP ta rahoto muku cewa, kotun ta sanya ranar Laraba 17 ga watan Afrilu, a matsayin ranar da Ganduje, da matarsa, Hafsat, da kuma dansa, Umar, za su gurfana a gabanta bisa zargin da gwamnatin kano ke musu na almundahana da kudaden al’umma.
Lokacin da maganar ta zo gaban Mai Shari’a Usman Na’abba, lauyan Ganduje, Nureini Jimoh, ya ce, ba a gurfanar da wanda yake karewa ba, don ba a mika masa takardar gayyata ba hannu-da-hannu ba.
Amma lauyansa, Nureini Jimoh ya kasance a kotun yayin da sauran wadanda ake tuhuma duk ba su halarci kotun ba.
Duba Nan: Kotu A Kano Ta Dakatar Da Ganduje Daga Shugaban Jam’iyyar APC
Lauyan gwamnatin jihar Kano, Y. A. Adamu, ya shaida wa kotun cewa, ba za su iya baiwa wadanda ake kara takardar gayyata hannu-da-hannu ba.