Bello Turji, hatsabibin shugaban yan bindiga a Zamfara, babu yadda za a yi gwamnati ta hana su samun man fetur idan har ta gaza hana su samun bindiga.
Turji ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi na musamman da yan jarida inda ya ke cewa ko karamin yaro ya san inda zai samu fetur Shugaban yan bindigan ya kuma yi koka kan yadda a cewarsa ake hana fulani shiga karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara, tare da hana su yin siyayyan kayan abinci.
Hatsabibin shugaban yan bindiga, Bello Turji, ya ce idan har gwamnati ba za ta iya dakile yaduwar bindigu ba a kasar, babu wanda zai iya hana yan bindiga siyan man fetur.
Turji ya yi wannan jawabin ne da ya ke magana game da dokokin da gwamnatin Jihar Zamfara ta saka a watan Satumban bara domin dakile ayyukan yan bindiga a jihar, rahoton Daily Trust.
Shu’umin dan bindigan ya yi jawabi ne cikin wata hira ta musamman da aka yi da shi a wani bidiyo da Trust TV ta wallafa mai lakabin ‘Nigeria’s Banditry: The Inside Story.
Idan za a iya tunawa, Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa su datse sabis a Jihar Zamfara da kewaye.
Yayin wannan lokacin, an rahoto cewa an kashe shugabannin yan bindiga da dama da yaransu yayin samamen da sojoji suka rika kaiwa a Jihar Zamfara. Idan an hana Fulani shiga Shinkafi, ina ke son su tafi – Turji
Bello Turji a zantawarsa da yan jarida Turji ya ce: “Ba daidai bane a hana Fulani shiga Shinkafi; karamar hukuma ce ta kowa da kowa. Idan ka hana Fulani shiga, ina ka ke son su tafi?
“Idan ka siya mudun masara, za su kwace; ko idan ka siya burodi, za su ce ka siya ne za ka kai wa Turji. Shin,Turji ne kadai ya ke cin abinci a nan? ”
Bari in tambaye ka; shin wannan ba bindiga bane? Shin wadand suka gaza hana yaduwar bindigu ne za su hana mu siyan man fetur, wanda ko karamin yaro ma ya san inda za a samu?”