Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya wanda shi ne babban manufar gwamnatinsa. (Albashi)
Shugaban wanda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin APC, karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Gwamna Hope Uzodinma, na Jihar Imo, a fadar gwamnati, ya ce gwamnatocin kasa da na kananan hukumomi za su yi aiki tare a kan mafi karancin albashin ma’aikata, wanda tuni y fara aiki.
“Muna bukatar yin wasu kididdiga da bincike a kan mafi karancin albashi.
“Dole ne mu kalli hakan tare, da kuma kudaden shiga. Dole ne mu karfafa tushe da kuma amfani da kudaden shigarmu, ”in ji shi.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai, Abiodun Oladunjoye ya fitar, shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin da su yi amfani da damar da aka basu na zabar su a cikin miliyoyin al’ummar jihohinsu domin kawo sauyi a rayuwar jama’a, inda ya kara da cewa zai yi aiki da su domin amfanar da ‘yan Nijeriya.
“Wannan taron ba bakon abu bane a gare ni, kuma abubuwan da taron ya kunsa yana da matukar amfani. Wannan ya shafi aikin Nijeriya ne ba Bola Tinubu ba,’’ in ji shi.
Shugaban ya ce za a daidaita yawan kudaden musaya.
“Na gaji kadarori da kuma bashin wanda ya gabace ni. Wannan shi ne karon farko da muka shiga zauren majalisa, kuma wannan ne karo na farko da zan yi taro.
“A matsayinku na masu kawo ci gaba kuma masu tunani a karkashin inuwar jam’iyyar APC kuna da rawar da za ku taka wajen wayar da kan jama’armu da kuma tabbatar da cewa mun gudanar da aikinmu yadda ya kamata,” in ji shugaban.
Shugaba Tinubu ya ce wannan alama ce mai kyau da karfafa gwiwa cewa jam’iyyar APC na da rinjaye a Majalisar Dokoki ta kasa da wasu Majalisun dokoki, wanda hakan zai sa a samu sauki wajen samar da manufofin da za su shafi tattalin arziki da jama’a kai tsaye.