Kungiyoyin Kwadago na Nijeriya, NLC da TUC reshen jihar Jigawa Sun Ki Amincewa Da Karin Albashin Naira 10,000 da gwamnatin jihar ta shirya fara biya a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin mai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan taron kungiyar kwadago ta jihar da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabannin kungiyoyin NLC da TUC tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin ta bayyana sanarwar da gwamnatin jihar ta yi na bayar da karin albashin ma’aikata a matsayin yarjejeniyar da ba a cimma matsaya ba.
Sanarwar ta ce, kwamitin tattaunawa na NLC kan karin albashi ya dade yana turawa jami’an gwamnatin batun tattaunawa kan karin albashin amma babu wata amsa.
Kungiyoyin Kwadago na Nijeriya, NLC da TUC reshen jihar Jigawa sun yi watsi da batun biyan karin albashin Naira 10,000 da gwamnatin jihar ta shirya fara biya a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin mai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan taron kungiyar kwadago ta jihar da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabannin kungiyoyin NLC da TUC tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin ta bayyana sanarwar da gwamnatin jihar ta yi na bayar da karin albashin ma’aikata a matsayin yarjejeniyar da ba a cimma matsaya ba.
Sanarwar ta ce, kwamitin tattaunawa na NLC kan karin albashi ya dade yana turawa jami’an gwamnatin batun tattaunawa kan karin albashin amma babu wata amsa.
Source: LEADERSHIPHAUSA