Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce sanar da yankin da ‘dan takarar shugaban kasar zaben shekarar 2023 zai fito ne zai nuna makomar Jam’iyyar su ta PDP mai adawa a zabe mai zuwa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar na daga cikin ‘yayan Jam’iyyar PDP da ke shirin shiga takarar zaben na shekara 2023, yayin da ake hasashen cewar Jam’iyyar na iya bai wa yankin kudancin kasar damar tsayar da ‘dan takara, ganin cewar mulkin Najeriyar zai cika shekaru 8 a hannun shugaba Muhammadu Buhari da ya fito daga yankin arewa.
Atiku ya ce a shekarar 2003 gwamnonin PDP sun sa shi tsayawa takarar domin hana shugaba Olusegun Obasanjo zarcewa, amma yaki tsayawa, abinda ya bai wa shugaban damar samun nasara.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce babu wani abu da ake kira shugaban kudancin Najeriya ko kuma shugaban arewacin Najeriya, sai dai shugaban Najeriya kawai, saboda haka matakin da jam’iyyar za ta dauka ya na da matukar tasiri dangane da makomar ta.
Rahotanni sun ce Jam’iyyar PDP ta bai wa Yankin arewacin Najeriya damar fitar da dan takarar shugabancin ta, abinda ke nuna cewar ‘dan takarar shugaban kasa na iya fitowa daga yankin kudu.
Jam’iyyar PDP ta kwashe shekaru 16 tana jagorancin Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2015 kafin APC ta raba ta da mulki.
A wani labarin na daban hukumar zaben Najeriya tace babu gudu babu ja da baya dangane da shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ake saran gudanar da shi ranar 6 ga watan Nuwamba duk da barazanar dake zuwa daga kungiyar ‘Yan awaren IPOB na hana zaben.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu yace babu dalilin ‘dage shirin gudanar da zaben domin sun tattauna akan irin barazanar da suke fuskanta da kuma hanyoyin da ake saran shawo kan su.
Yakubu wanda ya bayyana takaicin sa akan yadda ake ci gaba da fuskantar rasa rayuka da kuma kadarori sakamakon ayyukan ‘Yan awaren, yace ganawar da suka yi da bangarori da dama a Jihar Anambra ta nuna musu bukatar ci gaba da shirin gudanar da zaben wanda za’ayi a ranar 6 ga watan gobe.
Shugaban Hukumar zaben yace zasu ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaron kasa wajen gudanar da ayyukan su da kuma kare kayan aikin su, lura da yadda ake ci gaba da kai musu hare hare ana lalata su.
Ana saran Hukumar ta gabatar da kundin masu gudanar da zabe a ranar 7 ga wannan wata tare da kuma gabatar da sunayen ‘Yan takarar da aka tantance.