Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa na ranar ‘yancin kai na kasa, ya bayyana karin Naira 25,000 ga albashin kananan ma’aikata har na tsawon watanni shida masu zuwa.
A cikin jawabinsa da aka yada a fadin kasar a safiyar Lahadi, Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yanke shawarar karin albashin ne ga kananan ma’aikata na wucin gadi kafin ta zartar da tsarin mafi karancin albashi domin rage radadin hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Tinubu ya kara da cewa, gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin ta kauda matsananciyar rayuwar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, inda ya ce an dauki matakai daban-daban daga kowane mataki na gwamnati don dakile kalubalen.
Shugaban ya ce, gwamnatin kuma ta fito da wasu tsare-tsare da za su amfani ‘yan Nijeriya kai tsaye da za su rage musu radadin hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Shugaban ya ce, dangane da harkokin sufuri, za a samar da manyan motocin bas mai amfani da gas mai rahusa da aminci a fadin Nijeriya.
A wani labarin na daban gamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa, ta fara bayar da tallafin naira dubu ashirin-ashirin N20,000 ga ‘yan mata 45,000 domin tallafa wa harkokin karatunsu tare da karfafan iyayensu domin ci gaba da tura su zuwa makaranta.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan acikin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kan Nijeriya karo na 63 da ya gudana a dandamalin wasanni na Sani Abacha da ke birnin Kano.
Ya ce, “Domin agaza wa karatun yara mata da kuma karfafa wa iyayensu guiwa suke turasu zuwa makaranta, mun samar da wani tsarin tallafin naira N20,000 ga sama da ‘yan mata 45,000 a matsayin wani tsarin da zai ke taimaka wa harkokin karatunsu domin su cigaba da zuwa makaranta.
“Sannan, mun sake gabatar da tsarin motocin jigilar yara zuwa makaranta domin taimaka wa sufurinsu zuwa makaranta.”
Gwamnan ya kuma ce, gwamnatinsa ta na gina sabbin makarantu a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar a wani babban yunkuri da gwamnati ke yi na magance matsalar yaran da basu zuwa makaranta da suke gararanba a kan titina.
Kazalika, ya nanata aniyar tura daliban da suka kammala karatu da daraja ta daya (Fitst class) su 1,001 domin yin digirinsu na biyu a jami’o’in kasashen waje.
Sannan, ya ce, gwamnatinsa tana da muhimman tsare-tsare da shirye-shiryen da suka sanya a gaba da za su aiwatar a bangaren bunkasa harkokin koyo da koyarwa a jihar.
Source LEADERSHIPHAUSA