Shugaban na Rasha Vladmir Putin ya ce sannu a hankali Rasha tana nisantar kuɗaɗen kasashe marasa amana.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a yau Laraba a gaban babban taron tattalin arzikin Gabashin duniya karo na bakwai, a birnin a birnin Vladivostok na kasar Rasha, shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa, Kudaden ajiya irin su dalar Amurka da Yuro sun rasa amincinsu a matsayin tushen gishikin harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudade ta kasa da kasa.
“Kasashen yammacin duniya sun durkusar da ginshikin tsarin tattalin arzikin duniya, a irin wannan yanayi da kasashen turai suka shiga cikin dambarwa da rashin tabbas a harkokin tattalin arziki, akwai asara idan aka dogara da kudade irin su Dalar Amurka, ko Yurok o kuma Fam na Ingila.
Ya kara da cewa, wannan yanayi ta sa Rasha da sauran kasashe da dama su canza zuwa wasu kudaden na daban, musamman kudin kasar Sin, wato Yuan.
Mataki-mataki muna yin nisa daga yin amfani da waɗannan kuɗaɗen da ba abin doga ba ne hatta ma ga wasu kawayen Amurka, wadanda su ma yanzu sannu a hankali suna rage kudaden ajiyarsu da suka yi da kudin dala.
Putin ya ce yanzu haka, babban kamfanin iskar gas na Rasha wato Gazprom da abokan huldarsa na kasar Sin sun amince su yi mu’amalar kudi a tsakaninsu da ruble na Rasha da kuma yuan na China a cikin kashi 50% na hada-hadar kudadensu.
Source: ABNA HAUSA