Yayinda ake cigaba da fama da tsadar mai a birnin tarayya, Legas da wasu jihohi, NNPC tayi magana.
Gwamnatin tarayya na ikirarin cewa babu inda ake sayan man fetur da arha irin Najeriya a fadin duniya.
Shugaban NNPCL ya bayyana cewa ana barazanar kashe shi saboda kokarin da yake yi na gyara kamfanin.
Shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPCL, Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewa kamfanin ba zai iya cigaba da sayar da litan man fetur N170 ba.
Kyari ya bayyana hakan ne a taron da kwamitin yaki da rashawa na majalisar wakilan tarayya ya shirya a Abuja ranar Laraba, rahoton Punch. Ya ce yanzu kudin da suke sayo mai daga kasar waje ya ninka farashin da ake sayarwa har sau uku.
Yace: “Ba zai yiwu ka sayi mai N170, yayinda farashin da ake sayowa ya ninka hakan sau uku.”
“Misali yau idan man fetur ya shigo kasar nan, muna sayarwa yan kasuwa N113 ga lita domin ganin sun sayar N165.”
“Saboda haka dole mu sayar musu N113 don su sayar N165, haka na nufin cewa koma nawa muka saya, mu zamu biya raran.” “Babu inda zaka sayi mai a $1 (N445) a fadin duniya.
Hakan ba zai yiwu ba.
Shugaban na NNPC Mr Mele Kolo Kyari, ya ce yana ta samun barazana ga rayuwars sakamakon canje-canje da ake yi a NNPC.
A ccewarsa: “Ina so in ce cewa wannan masana’antar na kan bakin wata canji, akwai wata babbar canji da ke faruwa da kuma yana da tsada sosai ga mutane har da ni kaina.
“Akwai barazana ga rayuwata, zan iya fadan hakan, an yi barazana ga rayuwata sai da dama amma bamu damu da wannan ba, munyi imanin babu wanda zai mutu sai lokacinsa ya yi.
“Amma wannan ne farashin sauyi. Lokacin da mutane suka bar abin da suka saba da shi kuma suka fuskanci wani sabon abu da zai rage musu daraja da kuma samu da suke da shi, za su dauki mataki.
Hakan na da amfani ga dukkanmu kuma za mu yi aiki tare don tabbatar da cewa”.
Source:LEGITHAUSA