Yau asabar 18 ga watan Disamba Jamhuriyar Nijar tayi bikin cika shekaru 63 da zama Jamhuriya, inda a bana shugaba Mohamed Bazoum ya jagorancin shagulgulan zagayowar ranar a garin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar.
Bayan share tsawon shekaru ana gudanar da faretin soji da gabatar da wasannin gargajiya a irin wannan rana, to amma a shekara ta 2013, shugaban kasar na wancan Tandja Mamadou, ya sake fasalta yadda ake gudanar da bukukuwan, ta hanyar zabar daya daga cikin manyan birane don gudanar da ayyukan ci gaba da ake kaddamarwa a ranar ta 18 ga watan disamba.
Tun a shekara ta 2020 ne ya kamata a gudanar da bikin à garin Diffa, to amma aka jinkirta saboda dalilai na tsaro da kuma annobar covid-19.
Hakazalika a bana, an yi amfani da shagulgulan domin shirya wani kasaitaccen wasan kwalla kafa, Wanda ya hada tsoffin ‘Yan wasan Afrika irinsu Jeje Okaca, Hadj Diouf…… da dai sauransu.
Bikin na bana ya samu halartar mutane da dama ciki harda tawagar Najeriya wadda ta kunshi Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari.