Yan Najeriya da ke ajiyar kuɗaɗen su a wasu bankunan kasuwanci guda 20 da suka durƙushe suna da daman zuwa su karbi Kuɗinsu (NDIC)
Hukumar da NDIC ta bada tabbacin cewa babu wanda kudinsa zai yi ciwon kai kuma duk mai zuwa karban Kudi ya gabatar da ingantaccen shaida
Ɗaya daga cikin abubuwan da ke damun yan Najeriya masu ajiyar kuɗi a banki shine tabbatar da tsaron kudinsu
Hukumar kula da hakkokin masu ajiya a bankunan kasar nan (NDIC), da ke karkashin Ma’aikatar Kudi, ta kwato kudaden kwastomomi da ke ajiya a wasu bankuna 20 da suka durƙushe.
Bello Hassan, shugaban kuma babban direktan hukumar ne ya bayyana hakan yayin da ke jawabi a Abuja wurin taron bajekolin kasa da kasa.
Leadership ta rahoto cewa Hassan ya bayyana kwato kudaden da NDIC ta yi a matsayin cika alkawari da hukumar ta yi na cewa za ta kare kwastomomi idan banki ya durƙushe.
Shugaban na NDIC, wanda ya samu wakilcin direktan ayyuka a hukumar, Nuhu Bashi, ya yi alkawarin biyan kudaden baki daya ga duk wani kwastoma da ya taho don karban kudinsa.
Kalamansa:
“Abin da wannan ke nufi shine, domin jajircewar mu wurin sauya kadarori zuwa kudi, hukumar ta samu isasun kudi da za ta biya dukkan kwastomomi da kudinsu suka maƙalle a bankunan da suka durƙushe.”
Bankunan da abin ya shafa sune ABC Merchant Bank Limited; Allied Bank of Nigeria; Alpha Merchant Bank Pic.; Amicable Bank of Nig. Limited; Commerce Bank; Commercial Trust Bank Limited; Continental Merchant Bank Pic.: Cooperative & Commerce Bank Plc da Eagle Bank; Financial Merchant Bank Limited.
Saura sune Icon Limited (Merchant Bank); Ivory Merchant Bank; Kapital Merchant Bank Limited; Mercantile Bank of Nig. Plc.; Merchant Bank of Africa Limited; Nigeria Merchant Bank Plic.; Pan African Bank Limited; Premier Commercial Bank Limited; Progress Bank of Nigeria; da Rims Merchant Bank Limited.
NDIC ta yi kira ga masu ajiyar kuɗi, masu bada bashi, da masu hannun jari a bankunan da aka lissafa wadanda suka durƙushe su tafi kafafen da hukumar ta umurta su nuna shaida don karban kudinsu, The Guardian ta rawaito.
Hassan ya ce:
“An tura sakonni ga masu bada bashi na bankuna bakwai na ajiyar kuɗi (DMBs) da aka sayar da kadarorinsu da masu ajiyar kuɗi da tsaffin ma’aikatan ƙananan bankuna (MFBs) da bankunan samar da gidaje (PMB) su taho don karbar kuɗinsu da suka maƙalle a bankunan da suka durƙushe.
“Wanda abin ya shafa suna iya ziyartar ofishin hukumar mafi kusa da su ko su yi amfani da manhajar NDIC ta yanar gizo ko su ziyarci shafinmu na intanet: www.ndic.gov.ng, don bin hanyoyin yadda za su karbi kudinsu.”
Source:legithausang