Kudin Nijeriya a kasuwar musayar kudi ta bayan-fage ta karye, inda Naira 2000 take daidi da Fam 1 na Burtaniya.
Wani Mai canjin kudi a kasuwar ‘yan canji ta Wuse Zone 4 da ke Abuja, Malam Ibrahim, ne ya tabbatar wa da jaridar PUNCH da farashin a yau ranar Litinin.
Da aka tambaye shi game da canjin, sai ya ce, eh gaskiya ne, a halin yanzu muna canzar da sama da Naira 2,000 akan fam 1, kuma har yanzu ana kan bukatar wadannan kudaden.”
Sabon farashin ya karu daga Naira 1,930 da aka samu a ranar Asabar, kuma a halin yanzu shi ne mafi karanci a tarihin Naira.
Kazalika, darajar Naira ta fadi idan aka kwatanta da dala a kasuwar hada-hadar hannayen jari, inda ba a hukumance a kan same ta a N1,673 daga N1,670/$ a ranar Juma’a.
Ana ci gaba da samun wannan yanayin duk da yadda babban bankin Nijeriya ya aiwatar da wasu sauye-sauye da dama da nufin karfafa samar da kudaden waje.
Daya daga cikin sauye-sauye a baya-bayan nan shi ne sanarwar da CBN ta bayar na dakatar da kamfanonin mai na kasa da kasa da ke aiki a Nijeriya daga gaggauta tura kashi 100 na kudaden da suke samu ga kamfanoninsu a kasashen waje.
Manazarta kasuwar sun danganta koma bayan da aka samu a baya-bayan nan ga karuwar bukatar daloli tun farkon watan Janairu.
Source: LEADERSHIPHAUSA