Wani rahoton kwararru da aka tattara a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana yawan wadanda suka fada kangin yunwa ya karu zuwa kusan mutane miliyan 300 a shekarar 2023.
Rahoton ya ce karo na biyar kenan da ake fuskantar karuwar yawan mutanen da ke fuskantar yunwa a duk shekara tun daga shekarar 2019.
Rahoton ya dora alhakin karuwar matsalar yunwar a kan tashe-tashen hankula, iftila’in ambaliyar ruwa, fari sakamakon tasirin sauyin yanayi, sai kuma durkushewar tattalin arzikin kasashe da dama.
Ya zuwa yanzu mutane kusan miliyan 282 rahoton ya ce suna fama da yunwa a shekarar 2023.
Kazalika, ya ce an samu karin mutane miliyan 24 da suka fada cikin kangin yunwar, idan aka kwatanta da adadin da aka samu a 2022.
A wani labarin na daban rahotanni daga Jihar Kano, sun bayyana yadda aka shiga fargaba yayin da wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya fada kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar.
Wata majiya ta tabbatar wa Leadership Hausa cewa ginin ya rufta kan maginan da ke aikin fiye da 15.
Tuni dai masu aikin ceto suka fara zakulo mutanen da ginin ya rutsa da su.
Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutum daya daga cikin mutane uku da aka zakulo, yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali.
DUBA NAN: Kotu A Kano Ta Dakatar Da Ganduje Daga Shugaban Jam’iyyar APC
Sai dai ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga jihar, ko kuma adadin mutanen da suka rasu ko wadanda suka ji rauni.