Matatar man Dangote ta karɓi danyen mai ganga miliyan daya cikin miliyan shida daga hannun kamfanin mai na NNPC a ranar Alhamis.
A yanzu haka matatar na dab do soma tace mai da zarar ta kammala karbar ɗanyen mai daga NNPC.
Wannan dai na cikin yunkurin da Ɗangote ke yi na samar da wadataccen man fetur da samar da daidatuwar farashinsa kazalika da kuma samar da man a nahiyar Afirka ga baki daya, wanda wani yunkuri ne inganta tattalin arziki Nijeriya, kamar yadda Ɗangoten ya bayyana.
A makon da ya gabata ne dai kamfanin na Ɗangote ya karbi jirgi na hudu mai dauke da ganga miliyan ɗaya.
Ana sa ran mako mai zuwa za a kai sauran danyan man ganga miliyan daya wanda zai sa ya kai adadin miliyan shida idan aka hada da wanda aka kai wa matatar a baya.
Kuma da zarar an kammala kai man, kamfanin zai soma tace shi zuwa man fetur.
Matataar Dangote ta karbi danyen mai karo na hudu har ganga miliyan daya daga kamfanin man fetur na kasa (NNPC).
A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Lahadi, matatar ta Dangote ta ce tana sa ran samun danyen mai karo na biyar da za ta tace.
“Shirye-shiryen fara samar da mai a matatar Dangote na ci gaba da tafiya. Mun karbi danyen mai karo na hudu, ganga miliyan daya daga NNPCL kuma muna tsammanin karbar karo na biyar nan gaba kadan,” in ji kamfanin.
Dangote ya bayyana cewa da zarar matatar ta karbi jimillar ganga miliyan shida, za ta fara samar da man dizal, man jirgin sama, gas da kuma man fetur.
A cewar sanarwar, Manajan Daraktan Ayyuka na matatar Dangote, Akin Omole, ya sanar da ‘yan jarida cewa matatar ta yi hasashen samun kusan miliyan hudu a karshen shekarar 2023.
Matataar na sa ran karbar ganga miliyan biyu na danyen mai a farkon watan Janairun 2024.
A ranar 8 ga watan Disamba, 2023, Dangote ya sanar da karbar kashin farko na ganga miliyan daya daga kamfanin Stasco.
Haka kuma, a ranar 20 ga watan Disamba, 2023, matatar ta karbi kashi na biyu na danyen mai daga NNPC.
A ranar 29 ga watan Disamba, 2023, matatar Dangote ya ta sake karbar kashi na uku na ganga miliyan daya na danyen mai.
Source: LEADERSHIPHAUSA