Masara ta yi tsadar da ba a taɓa gani ba a Najeriya – Manoma
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar manoma ta Najeriaya AFAN ta ce ta damu da yanayin da aikin gona ke tafiya a damunar bana, inda ta ce hasashe ya nuna cewa amfanin da za a samu idan an yi girbi, mai yiwuwa ba zai kai na bara ba.
A hirar da BBC ta yi da sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Alhaji Muhammadu Magaji, ya ce amfanin gonar da za a samu bana zai kasance ne, kamar yadda na bara bai kai na shekara biyu da ta wuce ba.
Haka kuma, ƙungiyar ta ce har yanzu manoma ba su fara ganin takin da Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin samarwa a ƙasa ba, ga shi kuma damuna ta riga ta yi nisa.
Kimanin wata ɗaya kenan da wannan sanarwa ta shugaban Najeriya, lokacin da gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan wadata ƙasa da abinci.
Ƙungiyar manoma ta AFAN ta ce halin da ake ciki, abu ne mai tayar da hankali ga batun samar da abinci, ba ga al’ummar ƙasa ba kawai ba, har ma ga su kansu manoman, “domin a yanzu buhun sabuwar masara ya kai naira dubu hamsin da biyar zuwa sittin.
A cewarsa, bisa abin da suka saba gani a matsayinsu na manoma, kamata ya yi a ce buhun masara bai fi naira dubu goma sha biyar ba a wannan lokaci.
Alhaji Muhammdu ya ce, “ba wanda ya taɓa tsammanin samun haka, a ce a yanzu masara ta kai wannan farashin”.
Bincikin da BBC ta yi, ya nuna cewa, tsadar masarar ta shafi hatta masu kiwon gajin gidan gona.
Wani mai kiwon kaji ya ce, tsadar ta sanya buhun abincin kaji wanda a baya suke saye naira 600, ya tashi zuwa sama da dubu takwas a yanzu.
Sanadin tsadar abincin kajin kuma, farashin kiret din ƙwai ( ƙwai 30), kafin tsadar ana sayar da shi naira 1,700, amma a yanzu yana kai wa wajen N2,500.
Mai kiwon kajin ya shawarci gwamnatin tarayya ta gaggauta ɗaukar mataki kafin lamarin ya ƙara ɓaci.
“Maganar taki da ma jihohi ne suke (bayar) da taki, to ya kamata gwamnatin tarayya ta karɓi na jihohi, ta raba shi a matsayin tallafi,” in ji shi.
A bana takin zamani wanda manoma suka saba saye a farashin naira dubu takwas da ɗari biyar ya yi tashin gwauron-zabi, inda ya kai naira dubu ashirin da takwas.
Tsadar ta sa takin zamani a bana, ya gagari ɗumbin manoma masu ƙaramin ƙarfi.
Rashin wadatar taki da ma, abu ne da ya daɗe yana ci wa manoman Najeriya tuwo a ƙwarya, rashin samun sa a wadace kuma ne yake sa talakawa karkata ga takin gargajiya.
Wasu daga abubuwan da ke haddasa tsadar
Jami’in ƙungiyar manoman ya ce, abubuwan da ke haifar da matsalar raguwar abincin da ake nomawa, akwai maganar rashin tsaro, musamman a yankunan jihohin arewa maso yamma.
Wannan matsala ce da ta hana manoma da dama aiki sakamakon fargabar da suke yi ta zuwa gonakin da ke dazuka inda ake fama da masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Haka kuma a wasu yankunan na jihohi irin su Zamfara da Katsina da Naija, ɓarayin daji kan sace mutane su kai su, su riƙa musu aikin gona, baya ga sanya haraji da suke yi ga manoma a ƙauyuka.
Wata matsalar da ta janyo raguwar abincin a bana kuma in ji sakataren yaɗa labaran na ƙungiyar ta manoma, ita ce, tashin farashin mai a Najeriya.
Ya ce, ‘’a farkon watan shidan nan da manoma suka lura kuɗin mai ya karu wanda ya yi niyyar noma hekta biyar ya koma hekta biyu, wanda ya yi niyyar hekta goma ya koma uku ko biyar.
Matsala ta biyu kuma, ya ce ita ce ta talauci da tsadar rayuwa da ake fama da su a ƙasar, inda manoma ke sayar da ɗanyar masara, ɗanyen abinci, suke ɗauka suna amfani da su.
Ya ce, ‘’ka ga idan abinci zai maka wata shida ko takwas nan gaba, in ka fara cinsa yanzu to fa wata biyu wata uku ya ƙare.’’
Sai dai kuma masu hada-hadar masarar na cewa, daman akan samu ƙarancinta a irin wannan lokaci, saboda tsohuwa ta kare sabuwa ba ta zo ba.
Wani ɗan kasuwa a Dawanau da ke Kano da ke dillancin masara da wake ya ce a tsawon shekara talatin da ya yi a harkar kasuwancinsa, bai taɓa ganin masara ta kai naira dubu 30 ba a irin wannan lokacin.
Ya shaida wa BBC cewa, ”idan kaka ta yi dole farashin ya sauka amma ba lallai ne ya yi ƙasa a bana kamar yadda za a yi tsammani ba.”
Wani abu kuma da ake ganin ya taimaka wajen haifar da naƙasu ga damunar a bana shi ne rashin samun wadataccen ruwan sama a bana, inda ta kai wasu jihohin kamar su Borno da Gombe har ana addu’ar roƙon ruwa.
‘Za mu fara rabon tallafin taki a makon gobe’
A ranar 15 ga watan Yuli ne, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan wadata ƙasa da abinci, inda ta shigar harkar noma da albarkatun ruwa ƙarƙashin majalisar tsaron ƙasa.
Fadar shugaban Najeriya ta ce matakin wani martani ne ga hauhawar farashin abinci da ake fama da shi.
Cikin alƙawurran da gwamnatin ta yi akwai gaggauta bayar da taki da hatsi ga manoma da gidaje don rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Gwamnatin Najeriya ta ce nan da makon gobe za ta fara fitar da takin zamani don rabawa ga manoma a faɗin ƙasar. Babban mataimaki na musamman kan harkar yaɗa labarai ga Shugaban Najeriya, ya ce gwamnatin za ta fitar da takin zamanin ne inda za ta damƙa su hannun jihohi, su kuma su tsara hanyoyin rabar da su ga manoma.
Abdul’aziz Abdul’aziz ya ce an ɗauki wannan mataki ne saboda gwamnatocin jihohi suna da kusanci da al’umma, don haka su ne za su tsara hanyoyin rabon takin.
Ya ƙara da cewa takin, wani ɓangare ne na tallafi saboda bunƙasa harkokin samar da abinci don rage raɗaɗi kan wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fama da su bayan cire tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin ta yi.
Hanyoyin magance matsalar
Domin kare matsalar ƙarancin abincin da za a iya faɗawa ciki a najeriya, sakataren yaɗa labaran na ƙungiyar manoman ta Najeriya ya ce, kamata ya yi gwamnati ta ɓullo da ƙarin matakai cikin gaggawa.
Na farko ya ce, ya kamata gwamnatin tarayya ta karɓi abincin da ke hannun Babban Bankin Ƙasa, don sayar wa al’umma a jihohi cikin wannan lokaci.
Ya kuma ce “kada gwamnati ta shiga sayen kayan amfanin gona yanzu, maimakon haka tana iya bari sai an yi girbi don manoman ƙasa su amfana. Idan gwamnatin tarayya ta bayar da takardu yanzu a sayo, sai masara ta haura (naira) dubu 100, tun da tana dubu hamsin zuwa sittin a yanzu”.
“Bugu da ƙari, kamata ya yi kuma gwamnati ta yi shiri tun yanzu ta tanadi taki da sauran kayan noman rani, a raba su ga jama’a da zarar damuna ta tafi ta yadda za a shiga aiki ba tare da ɓata lokaci ba,” in ji shi.
Jami’in yana ganin idan aka tunkari noman ranin yadda ya kamata, abincin da za a samu zai taimaka wajen rage giɓin da za a samu a noman damuna.
Ya yi gargaɗin cewa muddin gwamnati ba ta hanzarta yin hakan ba, to akwai fargabar cewa al’umma za ta ƙara shiga mawuyacin hali na fatara da talauci da kuma yunwa a Najeriya.