A yayin da ake shirin shiga yin noma a kakar yin noma ta shekarar 2003, wasu daga cikin manoma a kasar nan, musamman kannan manoma, na ci gaba da yin korafi kan tsadar Irin noma, inda suka bayyana cewa, hakan na neman ya janyo masu babbar cikas akan sana’ar ta su.
Bisa rahotannin da aka samu, sun nuna cewa har ya zuwa yanzu, ma’aikatar noma da raya karkara ba ta riga ta sanar da shirye-shiyen samar da Irin noma a kakar aikin noma na bana ba.
Baya ga karuwar farashin takin zamani wanda ake sayar da shi daga naira 17,000 zuwa naira 20,000, haka tsadar ingantaccen Irin na kara zamowa manoma wani turniki, musaman ganin cewa, damina na kara karatowa.
Akasarin manoman dai, sun dogar ne a kan takin zamani da ingantaccen Iri don su samu amfanin gona mai yawa, sai dai, farashin kayan feshin a wasu kasuwanni, sun karu da kashi 100.
A yanzu haka dai, masa’antun da ke sarrafa shinkafa na bukatar sama da naira 60,000 domin sayen ingantaccen Iri da za su shuka a a kadada daya a kan naira 600 naira sabanin yadda aka sayar da shi a shekarar da ta wuce kan naira 400 na ko wane kilo daya, inda akalla manomi ke bukatar kilogiram 100 na irin da zai shuka a kadada daya.
Har ila yau, farshin ingantaccen Irin ya fi tsada, inda manoman ke ci gaba da nuna damuwar su kan hakan.
Wani manomin Masara a da ke a garin Zariya Haliru Hamza Kakaki ya nuna damuwarsa kan yadda farashin na Irin ya karau tun kafin a fara yin noman na bana.
Kakaki ya ci gaba da cewa, a cikin makon da ya wuce, kilogiram daya na Irin ya kai naira 600, mai makon farashinsa na naira 270 a shekarar da ta wuce.
Ya ce Irin Masara samfarin 510 wanda ake shuka shi da damina koda rani farshinsa ya kai naira 2,300 na ko wane kilogiram biyu wanda kuma zai iya bai wa manomi tan daga 5 zuwa 6, inda kuma Irin Masara samfarin 651 tsadarsa ta kai naira 1,800 na ko wane kilogiram biyu wanda za a iya samun daga tan 6 zuwa 7 a kadada.
Shi ma wani manomin Shinkafa Mista Ameh ya sanar da cewa, farashin Irin na Shinkafa mai nauyin kiligiram daya ya kai naira 600.
Ya kara da cewa, farashin Waken Soya samfarin 1904 da samfarin 1951 sun kai daga naira 700 zuwa naira 800 na ko wane kiligiram daya, inda kuma farashin Irin Rogo ya kai Naira 600 na ko wane kilogiram daya.
A jihar Neja kuwa, wani manomi mai suna Tanimu Doma ya bayyana cewa, farashin Irin ya karu a wannan shekarar iadn aka kwatanta da daminar rani ta shekarar data gabata.
Har ila yau, a jihar Kano kuwa binciken da Cibiyar amfanin gona ta kasa da kasa ta gudanar ICRI ta gano cewa, kilogiram daya na Irin Gero ana sayar da shi kan naira 600 na Masara ana sayar da shi kan naira 600 na Waken Soya ana sayar da shi kan naira 800, inda kuma ake sayar da na Wake kan naira 800.
Bugu da kari, a wasu kasuwannin binciken da aka gudanar ya nuna cewa, ana sayar da Irin Masara kan naira 750 zuwa naira N800, Irin Waken Soya ana sayar da shi kan naira 1,000, Irin Wake kan naira 1,000, Irin Shinkafa ana sayar dashi kan naira 1,300.
A bisa hasashen da manoma su k aka yi kana bin da ke farauwa na farashin Irin a wasu jihohin da ke a fadin kasar nan, manoman za su kashe kudade masu yawa wajen sayen Iri a kakar noman bana.
Wani manomi a kauyen Gofaru da ke a karamar hukumar Gezawa cikin jihar Kano Malam Surajo Baffa ya bayyana cewa, tashin farashin Irin na ci gaba da zamowa abin damuwa ga manonan da ke a jihar, musamman ganin cewa, ana shirin fara yin noman na daminar bana.
A jihar Katsina kuwa rahotannin sun bayyana cewa, manoma a jihar musamman kanana shekaru da dama da su ka wuce sundogar ne kan wajen sayo Irin da za su noma daga kasuwanni, ibda suke sayo Iri kamar na Wake, Waken Soya, Rogo Shinkafa da sauransu, amma sai dai, farashin wadanan amfanin , tuni ya kara yin tsada.
Har ila yau, bisa binciken da aka gudanar kan Irin Masara samfarin ‘Oba Super 6’ ana sayar da shi a kasuwannin Dandume, Funtua da Bakori kan naira 1,200 ko kuma kan Naira 1,500.
Wani mai sayar da Iri a kasuwar Gengere da ke a garin Jos, Auwalu Zaki ya bayyana cewa, kilogiram daya na Irin Shinkafa ana sayar da shi daga naira 600 zuwa naira 750 ya danganta da nau’in Irin.
A wata sabuwa kuwa, an bayyna cewa, ana samun kudaden shiga a kiwon Dan Akuya ko kuma taure kuma ba sai ka zuba kudade da yawa kafin ka shiga cikin fanin, haka wanda ya rungumi fannin, ya na bayar da gudunmwa wajen kara habaka tattalin arzikin kasa da kuma kara samar da wadataccen noma a kasar.
Kafin ka kawo ko wane irin Dan Akuya gida da zaka kiwata, ya wajaba kayi tuni kamar guda nawa ne ya kata ka sawo ka kawo gida don kaiwat wa, domin akasarin baban kuskuren da wadanda za su fara kiwata shi suke yi shi ne, yadda suke sayo su da yawa, su kuma kasance su kasa basu kulawar da ta dace, musamman wajen ciyar da su da kula da kiwon lafiyar su. Ya kamata ka fara da guda biyu kamar mace da namji, inda za su dinga haihuwa suna karuwa kadan-kadan.
Da farko ana bukatar ka samu wajen da zaka kiwat Dan Akuya, misali ga wanda yake da karfi zai iya kitwata kamar guda 200.
Farashinsa na da sauki idan aka kwatan-ta da a yankin Gabas ko kuma yankin yamacin kasar nan, inda farashinsa na jihohi kamar su Sokoto, Zamfara, Kebbi, Niger, Kaduna, Kano, Bauchi, da Yola, yake kai wa daga naira 7,000 zuwa naira 15,000, haka kiwon Dan Akuya wani fanni ne daka samun kudadne shiga ma su yawa.
Ana samun dimbin damarmaki a kiwon Dan Akuya kuma namansa na da dadi sosai, sai dai har yanzu mutane ‘yan kalilan ne suka yin kiwonsa a kasar nan.
Fanni ne da ake samun kudi a fadin duniya, musamman ga wadanda suke kiwata shi da yawa.
Rikakken Dan Akuya farashins na kai wa kimanin Fam 100 ya danganta da irin girman sa da yake da shi, haka idan ka kiwata Bunsuru guda 500 a shekara, za ka iya sayar da duk daya kan dala 150 ko zuwa dala 75,000.
Wanda zai fara kiwata Buinsuru ana bukatar ya fara tanadar wajen da zai gudanar da kiwonsa, haka ya danganta da yawan Bunsurai nawa zaka kiwata domin Bunsuru, dabbace da ki son tsafta.
Ana son wanda zai fara kiwata shi ya tabbatar da ya samar masa da dakin kwana domin Bunsuru bai son ruwa ya taba masa jiki ko kadan haka samar masa da dakin na kwana, na bashi kariya daga harbin cututtuka.
Ana kuma son a a dakin nasu na kwana su kasance nesa da nesa da juna don su dinga samun iska da kuma yadda za su samu sukunin yawata wa.
Akalla za ka iya ajiye Bunsuru guda goma a kadada daya idan kuma za ka ajeye guda 500, ana bukatar ka samu tanadi kadada 50, domin suna haihwa da sauri kuma da yawa.
Ana bukatar wanda zai fara kiwata su ya tabbatar da ya killace idan zai kiwata su kamar da waya ta karfe, musamman don gudun kar sauaran namun daji su shiga su yi masu illa.
Ana bukatar wanda zai fara kiwata Bunsurai ya tabbatar ya samo likitocin dabbobi da za su dinga duba amsa lafiyar su, musamman a lokacin da su ka kamu da wasu cututtuka, inda likitocin za su dinga zuwa don yi amsu Allura da kara duba ingancin lafiyarsu.
Za ka iya tuntubar Likitocin dabbobi na gwamnati ko kuma na masu zaman kansnu haka za su dinga baka shawara kan irin abincin da ya dace ka dinga basu kuma mai gina masu jiki don su yi saurin girma.
Ga wanda ke da bukata zai iya sawa a dibi maniyinsu don a zuwa wata dabbar kuma hakan zai sa dabbatar da aka zuba wa manin ta haifi da tamkar na Dan Bunsuru.
Source:LeadershipHausa