Babban Limamin kasar Mali da ya jagoranci zanga zangar adawa da gwamnati bara, Liman Mahmoud Dicko ya cacaki shugaban sojin kasar, Kanar Assimi Goita inda yake cewa al’amura basa tafiya daidai a cikin kasar.
Malamin yace basa tafiya tare shugaban sojin, kuma basa tafiya tare da kasashen duniya, saboda yadda ake nunawa kasar wariya.
A wani labarin kuma Mali ta sanar da cewa za ta jinkirta muhawarar kasa da take shirin yi a watan Disamba, zuwa wani lokaci da bata bayyana ba, matakin da ke zama sharadi ga gwamnatin kasar da sojoji suka mamaye a matsayin shirin komawa mulkin farar hula bayan juyin mulki har sau biyu.
To sai kuma kwatsam a wannan Talata kwamitin da aka kafa don shirya taron ya sanar da jinkirta shi, bisa cewa yunkuri ne na tuntubar bangarorin kasar da dama, ba tare da fayyace wa’adin gudanar da sabon taron na kasa ba.
Gwamnatin rikon kwarya ta Mali na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya na gaggauta maido da mulki ga fararen hula bayan da sojoji suka kwace mulki a watan Agustan 2020, sannan suka sake hambarar da wata gwamnatin farar hula a watan Mayu.
Bayan kwace mulki, kwamandan Sojin Mali Kanal Assimi Goita ya yi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabrairun shekarar 2022.
Sai dai da yawa na kallon jadawalin da shakku, ganin yadda gwamnati ke tafiyar hawainiya wajen shirye-shiryenta, da kuma yadda tashe-tashen hankulan masu ikirarin jihadi ke nesanta wasu yankunan Mali daga hannun gwamnati.